X

‘Najeriya na cikin ƙasashe 44 da ke buƙatar taimakon abinci’

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce farashin kayayyakin abinci ya ƙara tsada a watan Nuwamba, wata huɗu a jere. 

Hukumar ta ce an samu tsadar kayayyakin da kashi 1.6 a watan Nuwamba idan aka kwatanta da watannin baya. 

Hukumar ta ce wannan shi ne adadi mafi girma da aka samu a shekaru 10. 

Rahoton FAO ya ce rikici da fari ne suka ƙara haifar tsadar kayan abinci a wasu sassa na duniya musamman a gabashi da yammacin Afirka. 

Kuma rahoton ya ce ƙasashe 44 da suka ƙunshi 33 daga Afrika, da tara a Asia da biyu a Latin Amurka da Caribbean na buƙatar taimakon abinci daga waje. 

Ƙasashen da ke buƙatar abincin su ne Pakistan, Afghanistan, Bangladesh, Burkina Faso, Burundi, Kamaru, da Jam’huriyyar Afrika ta Tsakiya, Chadi, Congo, Korea, Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, Djibouti, Eritrea, Eswatini, Ethiopia, Guinea, Haiti, Iraƙi, Kenya, Lebanon, Lesotho, Liberia, Libya, Madagascar, Malawi, Mali, Mauritania, Mozambique, Myanmar, Namibia, Nijar, Najeriya, Senegal, Sierra Leone, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria, Uganda, Tanzania, Venezuela, Yemen, Zambia da Zimbabwe.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings