Najeriya: Jam’iyyar PDP na shirin babban taro na zaben sabbin shugabanninta
Bisa dukkan alamu rigimar cikin gida da ke addabar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya na ci gaba da yi mata tarnaki, yayin da a bangare guda shugabanninta da sauran masu fada a ji suke kokarin dinke barakar.
Kwamitin amintattun jam`iyyar ya yi wani zama na musamman a ranar Talata, inda ya bude zaurensa ga jiga-jigan jam`iyyar da kuma duka gwamnonin jam`iyyar su 13.

Sun tattauna a kan rikicin da ya dabaibaye jam`iyyar ne wanda ya ta’azzara musamman bayan da wadansu mataimaka ga `yan kwamitin gudanarwar jam`iyyar su bakwai suka yi murabus.
Dalilin murabus din shi ne ba su gamsu da jagorancin shugaban jam`iyyar na kasa, Uche Secondus ba, suna zarginsa da rashin iya shugabanci, suna kuma bukatar lallai ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai ya ce ba zai sauka ba domin babu laifin da ya aikata.
Wannan lamari ya jefa jam’iyyar cikin rudani da rashin tabbas.
Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taro na kasa kan shugabancinta
`Yan jam`iyyar PDP da dama dai sun yi tsammanin cewa a zaman kwamitin amintattun na ranar Talata, ne za a yi ta ta kare game da dambarwar da ake yi a kan jagorancin Mista Secondus, musamman ma maganar ko zai yi murabus ko kuma zai ci gaba da jagorancin jam`iyyar.
Sai dai kwamitin ya buge da maganar shirya babban taron jam`iyyar na kasa donmin zaben sabbin shuwagabanni, yana cewa za a mika duk wata matsalar jam’iyyar ga kwamitin zartarwarta domin dubawa.
Shugaban kwamitin amintattu na jam`iyyar ta PDP, Sanata Walid Jibrin ya shaida wa BBC cewa sun yarda cewa jam’iyyar zata ci gaba da kokarin tabbatar da hadin kanta ”ba tare da wani ya lalata ta ba.” Wannan ga alama fargaba ce kan yadda ricikin na cikin gida ka iya ruguza jam’iyyar ko kuma dakushe tasirinta.
Kawo yanzu dai jam’iyyar ta PDP ba ta bayyana ranar da za ta yi babban taron na kasa don zaben sabbin shuwagabannin nata ba amma ‘yan kwamitin amitattun sun ce ”nan ba da jimawa ba” za a yi taron.
Haka nan babu tabbas kan ko duka masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun yi na’am da shawarar gudanar da babban taron, ko kuma akwai wadanda za su sa kafa su shure shawarar.
To amma kwamitin amintattu na PDP ya ce jiga-jigan jam`iyyar sun yi nasarar daidaita tafiyarta domin kada ta fada cikin rami gabanin manyan zabuka na kasa da ake shirin yi nan da kasa da shekara biyu.

”An bai wa Uche Secondus zabi kan makomarsa”
Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin ya yi nuni da cewa taron nasu bai yi kokarin tilasta wa Mista Secondus ya yi murabus ba, amma kuma bai fayyace dalla-dalla matakin da suka bukaci shugaban jam’iyyar ya dauka kan makomarsa ba. Ya kara da cewa jam’iyyar tana ci gaba da duba matakan da za su kasance mafita a gare ta, amma ”mu ba mu ce wani shugaba ya je ya yi murabus ba ai.”
Duk da cewa jiga-jigan jam`iyyar ta PDP ba su fito kai-tsaye sun fadi shawarar da suka yanke a zaman da kwamitin amintattun ya yi kan makomar shugaban jam’iyyar na yanzu Uche Secondus ba, wata majiya a jam`iyyar ta tabbatar wa BBC cewa an ba shi zabi cikin abubuwa biyu.
Abubuwan kuwa su ne imma ya yi murabus daga mukamin nasa idan yana da niyyar sake neman wa`adin mulki na biyu, ko kuma ya karasa watanni uku da suka rage na wa`adin mulkinsa na yanzu sannan ya yi gaba.
Wakilin BBC Ibrahim Isa ya ce idan za a yi la`akari da take-taken jiga-jigan jam`iyyar ta PDP, za a iya cewa watakila Mista Secondus ya zabi karasa wa`adin nasa ne, tunda ana maganar shi ne zai jagoranci zaman da kwamitin zartarwar jam`iyyar zai yi a nan gaba.
A zaman na nan gaba ne za a kafa kwamitin da zai shirya babban taron jam`iyyar na kasa don zabar sabbin shugabanni.
Tushen sabuwar rigimar ta shugabancin PDP
Wannan rikicin dai ya fara ne da rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, wanda ya zargi shugaban jam`iyyar Mista Secondus da rashin iya shugabanci, har ta kai ga wasu gwamnoni da wasu manyan `ya`yan jamiyyar suka sauya sheka zuwa jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Daga nan sannu-sannu rikicin ya tasam ma raba kan gwamnoni da manyan jam`iyyar – matsalar da jiga-jigan nata masu korafi ke fargabar cewa za ta iya kassara jam`iyyar, a daidai lokacin da take bukatar tsayawa bisa duga-duganta don tunkarar babban zaben 2023. Wasu kuma na ganin rigingimu na da nasaba da batun tsayar da dan-takararta na shugabcin Najeriya a zaben na gaba, da kuma yankin da zai fito.
Kuma idan maganar kyale Mista Secondus ya kamala wa`adinsa ta tabbata, to zai kafa tarihi tare da kawo karshen kallon da ake yi wa kujerar shugaban jam`iyyar, wadda aka camfe cewa ba a gamawa da ita lami lafiya.
Cikin kimanin shugabanni 10 da ta yi daga 1999 zuwa yanzu, babu wanda ya yi saukar Allah da annabi – kowanne da rigima aka rabu da shi.
Jam’iyyar PDP dai ta mulki Najeriya tsawon shekaru 16 kafin jam’iyya mai mulki a yanzu wato APC ta doke ta a zabukan da aka yi a 2015.
A halin da ake ciki jam’iyyar ta PDP na fatan komawa kan mulki idan aka yi zabukan 20123, saboda a ganin ‘ya’yanta, jam’iyya mai mulki yanzu wato APC ta gaza biyan bukatun talakawa kuma ita ma tana da rigingimun cikin gida kan shugabancinta.
Sai dai masu sharhi na ganin rikicin cikin gidan na jam’iyyar hamayya ta PDP ka iya yi mata cikas gabanin zabukan, musamman idan ba a shawo kan rikicin ba.