Naira ta kara daraja zuwa N1260/$ a kasuwar chanji

Naira ta kara daraja zuwa N1260/$ a kasuwar chanji

Naira, a jiya, ta kara daraja zuwa N1,260 kan kowace dala a kasuwar kwatankwacin, daga N1,270 kowace dala a ranar Litinin.
Hakazalika, Naira ta kara daraja a NAFEM zuwa N1,262.85 kan kowacce dala.

Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa farashin canjin NAFEM ya ragu zuwa N1,262.85 kan kowace dala daga N1,278.58 a ranar Litinin, wanda hakan ke nuna darajar Naira 15.73.

Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin farashin kasuwa da NAFEM ya ragu zuwa N2.85 kan kowace dala daga N8.58 kan kowace dala a ranar Litinin.