Na matsu na sauka sabo da mulki akwai wuya – Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a jiya Litinin, ya bayyana cewa shekaru bakwai da ya yi a kan karagar mulki a matsayin “masu wuya”, yana mai cewa “na matsu na sauka.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulda da jama’a, Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC, ƴan majalisa da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.
Ya ce, “ Sarkin Daura, Dakta Faruk Umar, a filin idi ya gano cewa na yi watsi da tushe na. Ya rike lasifika ya na shaida wa kowa cewa tun 2021 rabon da na yi bikin sallah.
“Nan da watanni 10 zuwa 11, zan dawo nan. Ina da gida mafi kyau a Kaduna, amma ba zan zuna ba saboda kusancin sa da Abuja.”
“Na ƙagu na sauka da ga mulki. Zan iya gaya muku cewa gaskiya da wahala. Ina godiya ga Allah da mutane suka yaba sadaukarwar da muke yi. Ina yi wa wanda zai gaje ni fatan alheri,” inji shi.