Na koma rayuwa ta ta matar kwamandan mayakan Boko Haram : Aisha
Abin da ya sa na koma wajen ‘yan Boko Haram da kuma yadda na tsira’
A cikin jerin wasiku daga marubuta ‘yan Afirka, ‘yar jarida kuma mawallafiya Adaobi Tricia Nwaubani ta tattauna da wata mata kan zaman da ta yi tare da mayakan kungiyar Boko Haram cikin dajin da suke rayuwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A shekarar 2017, Aisha Yerima ta ba ‘yan uwanta mamaki bayan da ta koma hannun ‘yan Boko Haram da radin kanta bayan tun da farko sojoji sun kubutar da ita.
Shekaru hudu sun wuce kuma matar mai shekara 30 yanzu ta tsere kuma ta koma gidan iyayenta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An dai sace ta ne tun tana mai shekara 21 daga wani gari da ke kudu maso gabashin Maiduguri kuma an aurar da ita ga daya daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram, wanda ta ce soyayya ta shiga tsakaninsu saboda irin kyaututtukan da ya rika ba ta da son da ya rika nuna mata.
Wata rana bayan ya tafi yaki sai sojojin Najeriya suka kai wani samame a sansaninsu da ke dajin Sambisa, inda suka ceto Aisha da wasu gomman matan mayakan Boko Haram.
An kai matan wata cibiya wurin da ake sauya musu tunani na tsawon shekara guda, amma bayan watanni hudu, sai Aisha ta yanke hukunci cewa rayuwa tare da ‘yan Boko Haram ta fi mata dadi.
“Da kyar nake iya samun abin da zan gudanar da rayuwa ta,” kamar yadda ta shaida min. “Abubuwa sun yi min tsauri kuma tilas na dogara ga iyayena.”
Ta kuma sha wahalar ciyar da danta mai shekara biyu wanda ta haifa a sanadin auren kwamandan mayakan Boko Haram.
“Na kira mijina kuma ya yi farin cikin ji daga gare ni,” in ji Aisha.
“Ya shaida min ranar da zai zo Maiduguri domin sayen man fetur da gas, kuma mun shirya cewa zan bi shi.”
A ranar da suka ajiye, ta bar gidan iyayenta tare da dan nata, ba tare da sanar da kowa ba, kuma ta dauki tufafi kalilan ne.
Bikin harbi da bindiga
Ta ga mijin nata a wani boyayyen wuri kuma ya ba ta kudi domin ta sayo wasu sababbin tufafi, ta sake komawa wurinsa a wani wurin na daban da karfe 7.30 inda yake jiranta da wasu mayakan cikin wata motar bas.
Ta ce, “dukkansu na dauke da manyan bindigogi.”
Daga nan ne suka hau hanyar zuwa dajin Sambisa, inda suka yar da motar a wani gareji mai nisa, sannan suka ci gaba da tafiya a kafa.
Yayin da take da wani cikin wanda ya kai wata biyu, sai aka kashe mijin nata a fagen yaki.
Kamar wancan cikin shi ma wannan jaririn ya mutu yayin da take nakuda. Wannan batun ya gigita Aisha matuka.
An tilasta mata sake yin aure
Gadon da ta samu daga mijinta da ya mutu ya ba Aisha damar rayuwa mai kyau – sai dai wannan ya sa wasu sun fara jin haushinta.
“Sun rika cewa a wane dalilin aka bar ni ina jin dadina babu aure? Ban so na sake aure ba, amma sun tilasta min sai da na yi wani auren.”
Sabon mijin nata ma yana da kudi, dan kasuwa ne da ke safarar kaya daga Maiduguri zuwa sansanin ‘yan Boko Haram. Bayan ta sami wani cikin, sai Aisha ta yi fargabar zai sake mutuwa kamar sauran saboda rayuwar daji babu asibiti.
“Sai na roke shi cewa m koma Maiduguri, amma bai yarda ba.”
Daga nan ne fa zuciyarta ta koma ga barin wurin musamman da sojoji suka tsananta kai hare-hare ta sama, wanda ya tilasta wa mayakan sauya matsugunai.
Sai Aisha ta yanke shawarar tserewa.
Da karfe 3 na dare a watan Agusta, sai ta tsere tare da danta da wasu matan mayaka biyu wadanda su ma sun gaji da wannan rayuwar ta kunci.
Amma ‘yan Boko Harm sun kama su a kan hanya kuma sun mayar da su sansaninsu. Domin kar ta sake kokarin tserewa, sai mijin Aisha da mayakan Boko Haram suka kwace danta kuma suka kai shi wani wurin da ba ta sani ba.
Ta shafe kwanaki tana rokon mayakan su dawo mata da shi amma ba ta yi nasara ba. Da ta ga babu damar gani inda yake, sai ta yanke shawarar sake tserewa amma a wannan karon ba tare da shi ba.
Tsira da tausayawa
Wani mayakin da ya san hayar ficewa daga dajin ya amince zai nuna ma ta hanya tare da wasu mata fiye da 12 idan za su biya shi.
Aisha ta ba shi dukkan kudin da ta mallaka, kuma bayan mako guda ya yi musu jagora zuwa wani wuri a gefen dajin kuma ya nuna musu hanyar zuwa wani sansanin sojojin Najeriya.
Ta ce, “sojojin sun tausaya min kuma sun tara kudin mota wanda na yi amfani da shi na shiga mota zuwa gidan iyayena.”
Bayan sun isa Maiduguri, sai da ta tsayar da direban domin garin ya sauya, kuma ba za ta iya gane hanyar gidansu ba.
“Ko ina na duba sai sabbin hanyoyi masu kwalta da gadojin sama nake gani.
Dukkan ‘yan uwanta na jiranta a gida, kuma tana shiga kofar gidan sai suka rungume ta.
Aisha ta sanar da ni cewa tun bayan komawarta gida, kowa ya tausaya mata kuma su a taimaka mata.
Sai dai shi ma jaririn da ta haifa a farkon watan Oktoba ya mutu.
Kawo yanzu Aisha ba ta sami labarin mijinta da ta gudo ta bari a dajin Sambisa ba. Ta dai samu labari daga wasu matan da suka tsere daga can a kwanan nan cewa mayakan wani tsagi na kungiyar Boko Haram sun kama shi kuma babu wanda ya san inda yake.
Aisha ta kuduri aniyar gina sabuwar rayuwa, kuma tana fatan tara jarin yin kasuwancin turaren wuta da na fesawa.
“Ina rokon Allah ya tsirad da dana, amma ba zan sake komawa wurin Boko Haram ba,” in ji ta.