Mutum Biyu ne suka mutu a kasuwar GSM ta Beirut da ke cikin birnin Kano

Akalla mutane biyu ne suka mutu a wani bene mai hawa uku da ya ruguje ranar Talata a kasuwar GSM ta Beirut da ke cikin birnin Kano….
Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya a Kano Musa Abdullahi ya ce wutar lantarki ta kama wani jami’in kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) a yayin aikin ceto kuma ya mutu nan take.
Hakazalika, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum daya ya mutu daga cikin mutane takwas da aka ceto.
Hukumar NEMA ta bakin kodinetan ta na yankin Kano, Dr Nuradden Abdullahi, ya ce da misalin karfe 9:10 na daren ranar Talata, an ceto mutane 8 tare da garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammed.
“Abin bakin ciki, mutum daya ya mutu daga cikin wadanda aka ceto, an kuma yi wa mutane 6 da kananan raunuka magani kuma an sallame su, yayin da mutum daya mai karaya daya ke ci gaba da karbar magani,” in ji jami’in NEMA.
Har ila yau, hukumar kashe gobara ta Kano ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ta bayyana sunayen mutanen takwas da harin ya rutsa da su Naziru Abdulkadir mai shekaru 24; Magaji Abubakar, 27; Abdurauf Muhd, 38; da Minjibir Ibrahim mai shekaru 46; Ahmad Buhari Haruna, 16; Sadiq Haruna, 19; Abdurashid Basiru, 36; da Danladi Lawan, 29.
A halin yanzu, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya soke sunan filin ginin da ya ruguje.
Duk da cewa har yanzu ba a tantance masu ginin ba, hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta ce an yi amfani da kayan da ba su da inganci wajen ginin.
Gwamnan yayin da ya ziyarci wurin a ranar Laraba ya ce, “Da farko wannan wurin ya kamata ya zama wurin ajiye motoci kawai. Ya yi ƙanƙanta don ginin shago.”
Ya ba da umarnin a mayar da wurin zuwa filin ajiye motoci.
Ya kara da cewa za a kafa wani kwamitin fasaha da zai binciki musabbabin bala’in da ke nesa da kuma gaggawa.
“Ya kamata mu sani cewa daga farko, kowane gini ya kamata a tsara shi tare da kulawa da kwararru. A cikin mako guda wannan kwamiti ne kawai zai gabatar da rahotonsa kuma za mu yi aiki da shi yadda ya kamata,” inji shi.
Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su baiwa ma’aikatan da ke aikin tono tarkace hadin kai, inda ya kara da cewa, “Bayan an tono wurin yadda ya kamata, nan take gwamnati za ta fara samar da filin ajiye motoci da ya dace.”