Mutanen Magazu da Marke dake karamar hukumar Tsafe na yin kaura saboda azabar hare-haren ‘yan bindiga

Mazauna garuruwan Magazu da Marke dake karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara sun tattara nasu ina su sun yi kaura daga garuruwan saboda tsananin hareharen ‘yan bindiga.

jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa a cewa Wani mazaunin Magazu, Abubakar Magazu ya kwarmata wa wakilin ta cewa mutanen garuruwan na fama da tsananin hareharen ‘yan bindiga da yaki ci yaki cinyewa a yankin.

” Kusan kullum sai yan bindiga sun kawo mana hari. Ranar Laraba sun kawo hari inda suka sace mutane sama da 30 bayan an yi bude baki. Sannan suka farfasa shagunan mutane suka kutsa cikin gidajen mutane suka kwashi na kwasa.

” Bari in gaya maka ka sani a yankin mu yanzu babu wani gida da zaka iske suna da akuya biyu. duk ‘yan bindiga sun sace su kaf. 

A bisa haka ne gaba daya mutanen garuruwan suka tattara kayan su kowa yana yin kaura. Idan ka shiga garin yanzu zaka ga babu kowa a garin. Ana ta kwashe kaya ana kaura. 

Wani shugaban Matasa na yankin ya shaida cewa tun da safiya Juma’a ne mazauna garuruwan Magazu da Marke suke ta tururuwa zuwa hedikwatar karamar hukumar tsafe.

Idan ba a manta ba a cikin wannan makon ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kori wasu sarakuna biyu wato sarakunan Dan sadau da na Zurmi bayan bincike ya nuna suna da hannu dumu-dumu a rashin tsaro da ake fama da shi a fadin jihar.