Mutane 11 sun bace a Faransa sakamakon gobara

Mutane 11 ne suka bace bayan wata gobara da ta tashi a wani gidan hutu da ke karbar nakasassu a gabashin Faransa.


An aika kusan ma’aikatan kashe gobara 80 zuwa gobarar a Wintzenheim bayan an sanar da jami’an agajin gaggawa da karfe 06:30 agogon gida (05:30 BST) ranar Laraba.


Da alama an fara shi ne a wata kadara da wata ƙungiyar agaji ke amfani da ita wajen taimaka wa matasa masu nakasa.


An kai akalla mutum daya asibiti, bayan an kwashe mutane 17.


Da yake tabbatar da aikin ceto na ci gaba da gudana, ministan harkokin cikin gida Gérald Darmanin ya ce akwai yiwuwar an samu asarar rayuka da dama sakamakon gobarar da ta tashi a garin da ke kusa da kan iyakar Jamus.


A wata sanarwa da karamar hukumar ta fitar ta ce an shawo kan gobarar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.


Mutanen 11 da suka bace na daga cikin gungun mutane daga Nancy, da ke gabashin Faransa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.