Mun yi kutatacciyar rayuwa a hannun ‘yan bindiga — Wadda ‘yan bindiga suka sace

BBC – Wata mata da danta da wasu ‘yan bindiga suka sace a wani kauye da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, da kuma aka sako ta, ta ce sun sha bakar wuya a lokacin da suke hannun ‘yan bindigar.

Matar wadda BBC ta zanta da ita ta wayar tarho, ta ce,rayuwar da suka yi a hannun ‘yan bindigar sam ba dadi.

Ta ce,” Gaskiya ko abinci ba bu, idan ma an yi abincin sai dai kawai ka yi hakuri ka baiwa yaro, kai kuma kadan sanyawa bakinka kadan”.

A wasu lokuta da dama suna niko mana gari ne su kawo su ce muyi tuwo ko dambu, wani lokaci ko gishiri ba bu ballantana magi inji matar.

Ta ce abincin sau biyu kadai ake ba su, wato na safe da maraice, kuma sam ba ya kosar da su, sai dai kawai aci da hakuri, haka suma yaran ba sa koshi.

Matar ta ce, haka yara za su yi ta kuka saboda yunwa, amma su ko a jikinsu, sai dai su iyayen su yi ta lallashi har su hakura ko su yi bacci.

Ta kara da cewa, “Ga rashin wajen kwanciya mai kyau, ga mu muna cikin daji sauro da kwari irin damuna ma kadai su ishi mutum”

Matar ta ce, a lokacin da yake akwai sabis na waya, ‘yan bindigar da suka sace su kan ce musu su ba da lambar wani na su a kira, don a yi ciniki a kan kudin fansa.

To amma tun bayan da aka dauke sabis na wayar anan sun fuskanci tashin hankali sosai in ji ta.

Koda BBC ta tambayi matar wanne hali ‘yan bindigar da suka sace su suka shiga bayan da aka rufe kasuwanni?

Sai ta ce, sun fada musu cewa kasuwar da aka rufe an kara ja wa mutane, musammamma wadanda ke hannunsu.

Matar ta ce sun shafe tsawon kwanaki ashirin da shida a hannun ‘yan bindigar, amma kuma ba bu abin da suka yi musu kamar duka ko cin zarafi.

Ta ce,” Bana fata Allah ya kara maimaita min wannan bala’i, amma yanzu Alhamdullah tun da mun dawo wajen iyalanmu duk da yake muna gudun hijra saboda zaman kauyen namu ba zai yiwu ba a yanzu”.