Mohamed Bazoum: Makaman ƴan bindiga sun fi na sojojinmu
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum ya ce makaman da masu iƙirarin jihadi da yan bindiga suke amfani da su domin kai hari a kasarsa da ma yankin Sahel sun fi na sojojinsu.
Ya bayyana haka ne a yayin wani taro na ƙasa da ƙasa kan zaman lafiya da tsaro da aka gudanar a Dakar babban birnin Senegal.
Ya koka kan yadda masu iƙirarin jihadi ke ci gaba da ƙara ƙarfi a ƙasarsa da ma yammacin Afrika.
“Babu wani wuri a duniya da ƴan bindiga suka taɓa samun irin makaman da jami’an tsaron da ke yaƙi da suke amfani da su, amma ga shi a yau hakan na faruwa a yankin Sahel, ina ma tunanin wasu makaman da ƴan ta’addan ke amfani da su sun fi na jami’an tsaron,” in ji Shugaba Bazoum
Shugaban Nijar ɗin ya bayyana cewa sojojin ƙasashen Yammacin Afrika na buƙatar sabbin dabaru domin yaƙar masu iƙirarin jihadin da ke ƙara ƙarfi sakamakon saboda yalwatar fasahohin zamani ta ƙara bai wa yan bindigar wata dama a daidai lokacin da suke ƙoƙarin lalata yankin Sahel.
Yankin Sahel wuri ne da masu iƙirarin jihdi suke ƙara zafafa kai hare-hare da kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyi da muhallansu.
Ƙungiyoyi da ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS kamar su Boko Haram da ISWAP sun ƙara faɗaɗa a tsakiyar yankin na Sahel tun daga 2017 tare da ƙaddamar da hare-hare a Mali da Nijar da Burkina Faso da Najeriya.
Hare-haren da aka kai na baya-bayan nan a Nijar a ƙarshen makon da ya gabata shi ne wanda ƴan bindiga suka kashe aƙalla sojoji 12 yayin wata arangama a kudo maso yammacin iyakar ƙasar da Burkina Faso.
Ko a watan Nuwamba sai da gwamnatin Nijar ɗin ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu bayan da wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne suka kashe kimanin mutum 70.