Matatun man Port Harcourt, Warri za su fara aiki gabaɗaya a 2024

Matatun man Port Harcourt, Warri za su fara aiki gabaɗaya a 2024

Yayin da ake fama da karancin man fetur a Najeriya, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Man Fetur, Sanata Ifeanyi Ubah, ya ce matatun mai guda biyu – Fatakwal da Warri – za su fara aiki a karshen shekarar 2024.

Ya ce tuni aka tsara tsare-tsare domin cimma burin da aka sanya a gaba, inda ya ce matatar ta Kaduna za ta fara aiki kafin karshen shekara mai zuwa.

A cewarsa, kammala aikin da kuma kara samar da man fetur daga ganga 650,000 a kowace rana, matatar dangote na bpd zai baiwa al’umma damar biyan bukatar man da suke bukata a cikin gida.

Sanatan ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su dukufa wajen ganin an kafa matatun mai domin kara fadada karfin cikin gida na kasar nan wajen tace danyen mai.

Ya ce: “Aikina shi ne in tabbatar da cewa matatun mai a Najeriya sun tashi da aiki. Ta hannuna, kafin karshen wannan shekara, matatun mai guda biyu za su fara aiki

Haka kuma kafin karshen shekara mai zuwa matatar mai ta Kaduna za ta fara aiki. Har ila yau, za a samar da man fetur na jet, da tolubricant a tsakiyar shekara mai zuwa.

“Zan iya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba zan gaji ba tare da tabbatar da cewa wadannan matatun man sun fara aiki kafin karshen shekara. Mun kafa wata tawagar kwararru da za ta ziyarci matatun mai duk bayan mako biyu domin cimma burin da aka sa a gaba”.