Mata a Lagos sun yi murna da hukuncin da aka yanke wa tsohon dan sandan da ya yi wa yarinya fyade
Kungiyoyin kare hakkin mata da yara kanana a jihar Legas sun bayyana jin dadinsu kan wani hukunci da wata kotu ta yanke kan wani tsohon dan sanda a jihar.
Kotun ta samu dan sanda da aka kora Mohammed Alidu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, bayan samunsa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara tara fyaɗe.
Hajiya Ummul-Khairi Muhammad Agege na daya daga cikin shugabannin mata da ke jagorantar kungiyoyin fafutukar kare hakin mata da yara kanana a jihar Legas, ta ce wannan hukunci ya yi daidai da kiraye-kiraye da suke yi ga hukumomi a kasar.
Malama Ummul-Khairi ta ce da sauran hukumomi da sauran masu fada a ji za suke daukar irin wannan hukunci da lalle an samu saukin yi wa mata fyade ko kuma a kawo karshen ta’asar ma baki daya.
Ta ce yanzu haka suna da wata kara da suka gabatar a gaban hukumar kare hakkin yara da keta mutuncin mata bayan wani mutum da suke zargi ya yi wa wata budurwa fyade kuma ta samu ciki amma kuma yaki karbar yarinyar da aka haifa.
Tun farko dai a hukuncin da mai shari’a Abiola Soladoye ta yanke kan tsohon da sandan da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da gamsassun tuhume-tuhumen da aka yi wa wanda aka tuhuma ba tare da wata shakka ba.
Mai shari’a Soladoye ta lura cewa shaidar da ta bayyana kan abinda ya faru da yarinyar bayan binciken da likitoci suka gudanar ya wadatar cewa tabbas an keta mutuncinta.
A yanzu dai dan sandan wanda ya rasa aikinsa zai yi zaman fursuna na tsawon rai da rai ba tare da zabin tara ba.
Ta kuma kara da cewa ya kamata a saka sunansa a cikin rijistar masuyi wa yara kanana fyade a kundin gwamnatin jihar Legas.
Tun farko tawagar lauyoyin da suka gabatar da kara, karkashin jagorancin Misis Olusola Soneye, a lokacin sauraron shari’ar cewa wanda aka tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Yuni, shekara ta 2018 a Legas.
Misis Soneye ta ce Alidu ya yi wa yarinyar fyade bayan ya yi garkuwa da ita.
Lamarin ya faru a sa’ilin da take a kan hanyarta ta zuwa makaranta. Ya shigar da ita wani gidan katako kuma ya yi mata fyaɗe.
Wanda ya gabatar da kara ya bayyana-wa kotu cewa an kama wanda aka tuhumar ne bayan yarinyar ta kai rahoto ga ‘yan sanda game da abinda ya faru da ita.
Ta kara da cewa wanda aka tuhuma ya amsa laifin lalata da yarinyar wanda yace ya biyewa hudubar shaidan ce amma daga baya ya musanta hakan bayan da ya fahimci illar da hakan za ta yi ma sa a lokacin sauraron karar.
Mutum hudu ne suka bayar da shaida a kan dan sandan a lokacin da ake shari’ar.
Mai shari’a Soladoye ta ce wanda aka yanke wa hukuncin abin kunya ne ga ‘yan sanda saboda ya kasa bin doka da oda.