Masu kiran a raba Najeriya suna babban kuskure : Sunusi Lamido Sunusi
Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana cewa masu kiran a raba Najeriya suna babban kuskure.
A lokacin wani biki a Lagos wanda aka shirya domin taya shi murnar cika shekara 60 da haihuwa, Khalifa Sanusi ya ce akwai bukatar kasar ta kasance a dunkule sannan a gudanar da mulki cikin adalci a kasar.
Tsohon Sarkin Kano din kuma a cikin jawabinsa ya nuna takaici yadda wasu shugabanni a Najeriya ba sa mayar da hankali wajen ilimintar da al’umma.
A cewarsa bai wa bangaren ilimi musamman na ‘ya’ya mata muhimmanci shi ne zai kawo ci gaban kasa da kuma bunkasar tattalin Arzika.
A lokacin bikin, abokan Khalifa Muhammadu Sanusi sun tara makudan kudade domin tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya.
Tsohon Sarkin na Kano ya kaddamar da littafin makalolin da ya rubuta wanda kudin da aka tara su ne za a yi amfani da su wajen tallafa wa ilimi.
Ya kuma yi amfani da matsayinsa na jakadan majalisar dinkin duniya a kan muradun ci-gaba wato SDGs wajen jaddada bukatar masu hannu da shuni a kasar su tallafa wa ilimi musamman a yankunan karkara.
Gwamnoni shida ne sauka halarci bikin ciki har da na Kaduna da Lagos.
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote da gwamnan babban bakin Najeriya, CBN Godwin Emefele da wasu sarakunan gargajiya sun halarci bikin.
Shugabannin bankuna masu zaman kansu da kuma sarakunan gargajiya suma sun halarci bikin.