Masu jihadi sun fara shiga Benin
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya ce gwamnatinsa na daukar tsauraran matakai domin dakile kwararrar masu jihadi da ke kutsawa cikin kasarsa daga Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.
Shugaban da ke yin jawabi a gaban ‘yan majalisar dokoki a birnin Port Novo da ke a kudancin kasar, ya ce duk da matakan da suke dauka, a kwanan baya-baya nan a Porga kan iyaka da Burkina Faso masu jihadin sun kashe sojojin Benin guda biyu. Bincike wata kungiyar ta Clingendel da ke yin nazari a kan batun ta’addanci da ke da cibiya a Holland ya ce wasu ‘yan ta’addar na shiga Jamhuriyar ta Benin daga garuruwan kan iyaka tsakaninsu da Nijar da Burkina Faso da kuma Najeriya.