Masu garkuwa da mutane sun mamaye masallacin Taraba

Masu garkuwa da mutane sun kai hari a wani masallaci a Jalingo babban birnin jihar Taraba a ranar Alhamis, inda suka kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wani dan kasuwa da dansa.

Masu garkuwa da mutane sun kai hari a masallacin da ke Junction Jalo a unguwar Saminaka a cikin birnin Jalingo a lokacin da ake Sallar Magrib.

Dan hamshakin dan kasuwa ance dalibin Sakandare ne.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kashe mutane da dama ciki har da dan sanda guda tare da yin garkuwa da mutane sama da 30 a yankin cikin ‘yan watanni.

Masu garkuwa da mutane da ke gudanar da ayyukansu daga tsaunukan da ke kan kogin Lamurde a karamar hukumar Ardo_Kola, sun tilastawa mazauna yankin yin kaura.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bamu samu damar jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.