Masarautar Gumel ta Janye Salar Gani

Sallar Gani Wani Biki ne da Masarautar take yi a Duk shekara a cikin wantan Rabiul Auwal ma shekarar Musulunci, wanda bukukuwan sun kama da Hawa Dawakai da Sarakai suke yi gami da wasanni kala-kala kamar yadda ake bukukuwan Sallah a kasar Hausa

Sanarwar ta fito a jiya Laraba bayan Majalisar sararki ta zauana. Sanarwar ya fito kamar Haka

“Assalamu Alaikum. Gaisuwa da fatan alheri, bayan haka, dangane da zaman Majalisa na yau Laraba 28/9/2022, Majalisa ta janye bukukuwan Gani ta wannan shekara 2022, saboda tausayawa ‘yan uwanmu wadanda iftila’in ruwa ya shafa, musamman a Masarautun Hadejia, Ringim, Dutse da sauran yankuna na Jihar Jigawa da kasa baki daya. Wannan iftila’i yayi sanadiyar rasuwar mutane da dama, rushewar dubban gidaje, shafewar gonakai da sauran dukiya mai yawa. Allah Ya jikan wadanda suka rasu, Ya kuma mayarwa wadanda suka rasa dukiyar su da mafi alkhairi.

Don haka, za’a gudanar da addu’oi a wannan ranaku domin neman Ubangiji Ya kawo mana sauki akan dukkan matsaloli da suke damun mu, Ya yaye mana dukkan masifu, Ya kuma tabbatar mana, lafiya, zaman lafiya, da karuwar tattalin arziki a Masarautar mu, Jihar mu, da kuma kasar mu Najeriya baki daya

COUNCIL Allah Ya tabbatar mana da dukkan alkhairi, Ya bamu lafiya da zaman lafiya, Amin.”