Manyan Jiga-Jigan APC Guda 15 Sun Fice Daga Jam’iyyar a Kaduna

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ta yi rashin manyan jiga-jiganta har guda 15 a ranar Alhamis Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida, wanda ya samo asali daga zaɓen fidda gwani na gwamna Masu suaya sheƙan su bayyana cewa sun yi haka ne domin gujewa rikicin APC da kuma rashin ganin ƙimar mambobi

Kaduna – Manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressive Congress APC a jihar Kaduna su 15 sun fice daga jam’iyyar, inda suka kafa hujja da rashin demokaraɗiyyar cikin gida. Ɗaya daga cikin jigogin da suka fita daga APC ya shaida wa wakilin jaridar Punch cewa akwai mambobi 500 da zasu mara musu baya biyo bayan rashin shawo kan rikicin da ya addabi jam’iyya a jihar.

Sauran su ne; Samuel Wyah, Zaka Makoshi, Jonathan Fedelix, Barnabas Samuel (Barry), Shua’ibu Yusuf, Alexander Danladi (Lulu), da kuma Samuel Ibrahim. DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka Meyasa suka fice daga APC? Mai ba da shawari kan harkokin shari’a na APC a ƙaramar hukumar Jema’a, Honorabul Ibrahim Samuel, a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyya na gunduma, ya ce: “Na ɗauki matakin fita daga APC ne saboda rikicin cikin gida da rashin demokariɗiyyar cikin gida da rashin ganin mutuncin juna.”

Haka nan, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Barnabas Samuel da Hon. Ibrahim Samuel, wacce aka raba wa manema labarai ranar Alhamis, masu sauya sheƙan sun koka kan canza sunayen Deleget.

Sun yi ikirarin cewa banbancin da aka samu a sunayen ne ya jawo shari’ar da ake tafka wa a Kotu tsakanin Sanata Uba Sani da Sha’aban. A wani labarin kuma Tawagar mambobin APC sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP, Ɗan takara ya tarbe su hannu biyu a jiha ɗaya

Ɗan takarar gwamnan jihar Legas karƙashin inuwar PDP, Dakta Adediran, ya ce ya karbi mambobin APC da suka sauya sheƙa. Adediran, wanda ya bayyana sunan tawagar masu sauya shekan, ya ce sun bar APC ne saboda sun yarda da alƙawarin jam’iyyar PDP.