Makomar Messi bayan kawo karshen zaman shekaru 20 da Barcelona
Ranar da magoya bayan Barcelona suka dade suna fatan ganin bata zo a nan kusa ba ta cim musu a ranar Alhamis, bayan da ta tabbata gwarzon dan wasansu kuma kaftin dinsu Lionel Messi zai sauya sheka.TALLA
Lionel Messi zai kawo karshen zamansa na shekaru 20 tare da Barcelona ne bayan gaza cimma matsaya kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar, saboda cikas na tattalin arziki da da wasu matsalolin da suka rinjaye ta, kamar yadda ta sanar a ranar Alhamis.
Tun ranar 30 ga watan Yuli ne dai Lionel Messi ya kasance mai zaman kansa bar tare da wata yarjejeniya ba, sakamakon karewar da kwantaraginsa yayi da Barcelona.
A watan Agustan shekarar bara Messi ya yi kokarin barin Barcelona amma hakarsa ta gaza cimma ruwa, abinda ya haifar da tsamin dangantaka tsakaninsu bayan da kungiyar ta yi barazanar maka dan wasan a kotu saboda zarginsa da karya yarjejeniyar da suka kulla kan cewar sai a karshen kowace kakar wasa yake da damar rabuwa da ita, dan haka kama ta yayi ya sauya sheka a karshen watan Yuni ba Agusta ba, yayin da shi kuma ya dage kan cewar babu wata ka’ida da ya saba.
A waccan lokacin dai rahotanni masu karfi sun yi ta alakanta Messi da komawa Manchester City inda aka ruwaito cewar hatta mahaifinsa ma ya tattauna da wakilan kungiyar a Ingila.
Sai dai daga bisani bayan amincewa ya tsawaita zamanssa da shekara 1, Barcelona da magoya bayanta sun samu kwarin gwiwar kaftin din na su zai ci gaba da zama tare da su har zuwa shekarar 2026 lokacin da zai cika shekaru 39.
Messi mai shekaru 34 ya rattaba hannu kan kwantiraginsa na farko da Barcelona ne a shekarar 2000 lokacin yana dan shekara 13 kacal.
Bayan soma haska mata a matakin kwararru, Messi ya ci wa Barcelona jumillar kwallaye 672 cikin wasanni 788 da ya bugawa kungiyar.
Wani tarihi da Messi ya kafa mai wuyar gogewa a Barcelona shi ne cin kwallaye sau uku-uku da ya rika yi a wasanni har sau 53, abinda ya sa masana a duniyar sarrafa tamaula ke ganin akwai babban kalubale gaban Barcelona kafin ta samu nasarar cike gibin da tsohon kaftin din nata zai bari ta bangaren cin kwallaye.
A bangaren Kofuna Messi ya taka gagarumar rawa wajen daga darajar Barcelona inda ya taimaka mata wajen lashe jumilar kofuna 35 daga cikinsu har da na gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Turai 4.
To wani abu da ke daukar hankali kuma shi ne a yayin da manyan kungiyoyi masu abin hannu ke fatan samun nasarar kulla yarjejeniya da Lionel Messi, za a iya cewa burin abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya cika, domin kuwa Ronaldon ya taba kalubalantar Messi da cewar idan ya isa shi gwarzo ne to ya bishi gasar Seria A ta Italiya, inda ya koma Juventus bayan raba gari da Real Madrid a shekarar 2018.
To har yanzu dai babu wata kungiya da ta tabbata cewa ita Messi zai koma, sai dai ana kyautata zaton Paris Saint German ke kan gaba sai kuma Manchester City, wadanda aka shafe watanni ana alakanta su da gwarzon dan wasan.
Ga kungiyoyin da ke neman kulla yarjejeniya da Messi sai dai mu ce ba a san maci tuwo sai miya ta kare, ga kungiyar Barcelona kuwa tsohuwar karin maganar nan ce dai ta “Sai yadda ta yiwu nakuda a dakin mayya” duba da irin gibin da Leo ya bar musu.