Makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Wani bidiyo ya karada shafukan sada zumunta da sunan an yi ram da ‘yan bindiga a Kaduna, Binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya tabbatar da cewa wasu makiyaya ne kurum aka kama Rashin fahimta ya jawo rigima ta barke tsakanin Fulani da wasu mutane, har aka rasa rayuka a Chikun

Sojoji da ‘yan sanda sun yi bayani game da bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta, da sunan cewa an kama ‘yan bindiga a jihar Kaduna. A wani rahoto da ya fito a jaridar Leadership ta ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu 2022, an ji cewa ba ‘yan ta’adda aka kama kamar yadda mutane su ke tunani ba. Jami’an tsaro sun yi wannan karin haske yayin da aka yi wani zaman sulhu tsakanin jagororin Gbagyi da kuma al’ummar Fulani da ke Kakura a garin Chikun.

A cewar jami’an tsaron, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mutanen da aka gani a bidiyo, makiyaya ne aka yi ram da su, ana tunanin ‘yan bindiga ne. ‘Yan banga ne suka yi kuskuren damke wadannan mutane, bisa zargin cewa su ne ‘yan bindigan da suka kai wa mutanen Kakura farmaki babu gaira-babu dalili. An yi taro a ofishin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shugaban karamar hukumar Chikun, Salasi Musa sun samu halartar wannan zama.

Sauran wadanda aka yi taron da su, sun hada da ‘dan majalisar yankin Chikun, Hon. Ayuba Chawaza, Hakimin Kujama, Stephen Ibrahim da jami’an tsaro. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, Yekini Ayoku ya shaidawa mahalartan cewa an taba mutanen Gbagyi da na Fulani a harin da aka kai a ranar Asabar.