Majalsar wakilai ta sanya a yi bincike game da cunkoso a gidajen YARI

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta mai kula daukumar gidajen yarin ƙasar ya gudanar da bincike kan yanayin da ake tsare mutane a Najeriya.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar ne ya gabatar da wata buƙatar gaggawa inda ya nuna damuwa kan mummunan yanayin da ma’aikatan gidajen yari ke aiki, da kuma halin ƙunci da fursunoni ke ciki.

BBC ta ruwaito cewa Honarabul Kabiru Alhassan Rurum ya shaidawa Mata cewa na dauki matakin ne domin yin gyara a harkokin da suka shafi gidajen kason, duba da yadda suke cunkushewa da marasa laifi.

Sannan ya ce akwai abin takaci ganin yadda ake cika fursunoni a daki guda, inda mutum 10 ya kamata su kwana sai ka an samu sama da mutum 50 a ciki.

Majalisar ta kuma kara da cewa, akwai bukatar tabbatar da za a maida gidajen yarin na gyaran hali, maimakon zamo wa wurin sake koyon lalata, sakamakon yadda ake gwamutsa masu kananan laifi da muggan laifuka.

”Yanayin da gidajen yari ke ciki da fursuna da ma’aikata abu ne da duk dan kasa na gari sai ya yi allawadai da shi, abubuwan da ke faruwa a gidajen yari a birni da kauye duk daya ne,” in ji Rurum.

‘Bahaya a wajen kwana’

“A wasu wuraren za ka samu bandaki daya ne, ko kuma za ka samu inda mutanen ke kwana nan suke bahaya da sauransu.

Wannan na daga cikin dalilan da ke yawan sa ake samun rahotannin kai hari gidajen kaso, domin kubutar da wadanda ke ciki komai girman laifinsu”, in ji Dan majalisar

Alhassan Rurun ya ce wannan shi ya sa mai gabatar da kudurin ya yi kira ga majalisa ta amince a kuma bai wa kwamitin da ke kula da gidajen kason Najeriya damar gayyato masu kula da gidajen yarin, da zagayawa domin gani da ido da lalubo hanyar magance matsalar.”

Ɗan majalisar ya kuma kara da cewa, a tabbatar za su maida gidajen yarin na gyaran hali, maimakon zamowa wurin sake koyon lalata sakamakon yadda ake gwamutsa masu kananan laifi da muggan laifuka.

Akan batun makaman da ake bai wa masu aikin gidajen kaso kuwa, Rurum ya ce babu isassun kayan aiki kuma ba a zamanantar da aikin na su, sannan idan an ware kudi a kasafin kudi babu abin da ake yi da su.

Karin haske

Buƙatar gyaran gidajen kason Najeriyar na zuwa ne kwana guda bayan wani rahoto da BBC Hausa ta gabatar, da ya bankaɗo halin taɓarɓarewar da gidajen yarin Najeriya suke ciki.

Akwai fursunoni kusan 70,000 a gidajen yari a Najeriya, sai dai kimanin kashi 75 cikin 100 ‘yan zaman jiran shari’a ne.

Wasu fursunonin kan kwashe shekara da shekaru ba su san matsayinsu ba, wasu ma kan shafe shekarun da suka zarta tanadin da doka ta yi na hukunci mafi tsanani na laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Wasu ɗaurarrun kan ma rasa rayukansu a lokacin zaman shari’a a gidajen kason da ke jihohi daban-daban a kasar.

Alkaluma na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa akwai fursunoni fiye da miliyan 11 a gidajen yari a fadin duniya.

Fiye da miliyan uku daga cikinsu ana tsare da su ne ba tare da an yi masu shari’a a kotu ba, bare a yi batun hukunci.