Majalisar Dokokin Najeriya Ta Amince Da Sabuwar Dokar Zabe Da Ta Yi Wa Gyaran Fuska

A wannan karon an amince da zaben ‘yar tinke, ko ta wakilan jam’iyyu ko ta sulhu amma akwai karin gyara da ya shafi kwarewar ‘yan takara.

Majalisar dokokin kasa da ta kunshi ta dattawa da ta wakilai ta amince da gyara sashi na 84 na sabuwar dokar zabe, inda suka amince da abubuwa uku, wato zaben ‘yar tinke, da ta wakilan jam’iyyu ko delegate a turance da kuma zaben dan takara ta hanyar sulhu.

Kafin wannan lokaci da aka cimma wannan daidaito, majalisar wakilai ba ta amince da zaben dan takara ta hanyar sulhu ba. Amma yanzu ta amince.

“Mun yi dan gyara cewa in ma an ce maslaha ne, to ba za a zo kawia a yi kama karya ba.” In ji Shugaban Kwamitin Kula da harkokin Hukumar Zabe a Majalisar dattawa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Ya kara da cewa ba su amince jam’iyya ta kawo dan takara da bai cancanta ba ko ba shi da ilimin da bai kai ba.

Shi kuwa Shugaban Majalisar, ba da shawara ta Kungiyar Jam’iyyun Najeriya 18 Yabagi Yusuf Sani ya ce dama dimokradiyar Najeriya ba ta yi Karfin da za a yi zaben yar tinke ba.

Majalisar dokoki ta aikawa Shugaba Mohammadu Buhari da sabuwar dokar zabe da a yanzu ta tashi daga dokar zabe ta 2021 zuwa dokar zabe ta 2022.