X

Majalisa ta miƙa wa Buhari ƙudirin dokar zaɓe da ta yi wa kwaskwarima

Majalisar Dokokin Najeriya ta miƙa ƙudirin dokar zaɓe da suka yi wa kwaskwarima ga Shugaba Muhammadu Buhari don ya sanya mata hannu. 

Mai taimaka wa Buhari kan harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Babajide Omoworare, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Litinin. 

Ya ce miƙa wa shugaban ƙasar ƙudirin ya dace da sashe na 58 (3) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, yana mai cewa Akawun Majalisa Olatunde Ojo ne ya aika da kwafin kuɗirin a ranar Litinin. 

A watan Disamba ne shugaban ya ce ba zai saka wa dokar hannu ba har sai an gyara sashen da ya tilasta wa jam’iyyun siyasar ƙasar yin zaɓen ‘yar tinƙe wajen fitar da ‘yan takara, yana mai cewa sai an ba su zaɓi. 

Bayan dawowarsu daga hutun shekara, majalisun tarayyar sun gyara dokar tare da bai wa jam’iyyun zaɓin ‘yar tinƙe da zaɓen wakilai da kuma masalaha. 

Da zarar Buhari ya sanya mata hannu ta zama doka. Ita ma hukumar zaɓe ta INEC ta ce da ma abin da take jira kenan kafin ta fito da jadawalin babban zaɓe na 2023.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings