Maina Ya Shafa Wa Dansa Kashin Kaji
A jiya ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke belin da ta bai wa Faisal Maina, dan Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Farfado da Tara Kudin Fansho na Kasa, tare da bada umarnin a kamo shi bisa gaza bin ka’idojin belinsa kan tuhume-tuhumen da a ke yi ma sa na harasta kudin haram.Alkalin Kotun, Mai Shari’a Okon Abang, shi ne ya bada wannan umarnin yayin da ya ke cewa, kotun za ta cigaba da sauraron shari’ar gabanin jami’an tsaro su samu nasarar cafko shi tare da tuso keyarsa zuwa gabanta.Sannan kotun ta bukaci wanda ya tsaya wa Faisal a lokacin beli, wato mamban da ke wakiltar mazabar Kaura-Namoda a Majalisar Wakilai ta kasa daga Jihar Zamfara, Hon. Sani Umar

Dangaladima, da ya bayyana a gabanta gami da yi ma ta cikakken bayanin dalilinsa na gaza kawo wanda ya sanya hannu wajen amsar belinsa a hannun nata.Umarnin kamo Faisal Maina na zuwa kasa da kwanaki shida da wannan kotun ta bada wani umarni makamancin wannan na cewa a kamo mahaifinsa a duk inda a ka yi tozali da shi bisa kin dawo wa gaban kotun da ya yi, wanda hakan ya sanya kotu soke izinin belinsa tare da neman a sake kamo shi. Haka nan kuma, kwana guda kenan da ta tsare Sanata Ali Ndume, a gidan kurkuku bisa tsaya wa mahaifin Faisal din a matsayin mai amsar belinsa, bayan da ya kasa bayyana a gabanta yayin da zaman da ta yi.Baban nasa dai, wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin hukumar farfado da tara kudaden fansho, ya na fuskantar tuhuma ne kan zargin badalakar Naira biliyan 2.1.A ranar Litinin ne dai Alkalin Okon Abang, ya tura mai tsaya wa Maina wajen beli, Sanata Ali Ndume gidan yari da neman sa da ya kawo wanda ya tsaya masa domin fitar da kansa.Tun bayan hukuncin neman kamo Maina, kotun ta cigaba da zamanta ba tare da bayyanarsa a gabanta ba.A zaman kotun na jiya Talata, Lauyan da ke tsaya wa hukumar EFCC Mohammed Abubakar ya shaida wa kotun cewa Faisal da wanda ya amshi belinsa duk sun ki zuwa gaban kotu tun wani zama da kotun ta yi a ranar 24 ga watan June, 2020.Har-ila-yau, Faisal, mai tsaya masa kan beli ko Lauyansa duk babu wanda ya halarci zaman kotun na jiya.Kan haka ne, lauyan na EFCC ya shigar da bukata a gaban kotun ta neman ta soke belin Faisal tare da umartar a kamo shi bisa dogaro da sashe na 184 na Dokar Gudanar Da Manyan Laifuka (Administration of Criminal Justice Act).