‘Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, a gyara’ : Sheikh Gadon Kaya

Sheikh Gadon Kaya ya bayyana cewa wasu ma’aikatan lafiya ne suka fara tuntuɓarsa kan wannan lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama’a.
“Wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu, namiji da mace ne suka kira ni, muna karatu ne suka yi min fatawa, inda suka fadi matsalar da suke fuskanta ta haɗa mace da namiji, wani lokacin a cikin aiki na dare.
“Suka koka, kuma na yi bayani a matsayina na almajiri, mai nusantar da mutane akan aikata daidai.”
Ya ce ya yi bayani ne cewa matukar hakan na faruwa ya kamata a gyara: “Ya kamata a tsare mutunci matan nan da iyalanmu da ‘ya’yanmu gaba ɗaya.”
Sheikh Gadon Kaya ya ce bayan da kalaman nasa suka tayar da hankalin jama’a, musamman ma’ikatan lafiya, ya zauna da su, inda ya ce “sun warware min dukkan abubuwan da suka shige min duhu kan wannan lamarin.”
Ya ce ma’aikatan lafiyan sun “yi gungu kuma sun ziyarce ni”.
Ya kuma ce sun sanar da shi cewa labarin da ya yada babu ƙamshin gaskiya cikinsa, kuma ya ce ya hujjarsa ita ce “wasu ma’aikatanku ne suka kira ni, suka tambaye ni a karatu kuma na bayar da jawabi, inda na ce a gyara”.
“Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, na ce a gyara.”
Ya ce bayan da suka “yi min bayani, kuma na yi musu bayani, mun fahimci juna. Sai na ce mu su ‘ba ku fahimci maganganun da ake yadawa ne ba’.”
Ya kuma yi karin bayani, inda yace dalilinsa na biyu na furta wadannan kalaman masu tayar da hankali shi ne domin yana cikin masu yin kira ga al’umma da a rungumi karatun kiwon lafiya domin saboda akwai bukatar su cikin al’ummar kasar.
Shehin ya ce bayanan da ma’aikatan lafiya suka yi kan batun, ya ƙaru da wasu abubuwan da a baya bai sani ba.
Sai dai ya kare kansa inda ya ce bai ambaci sunan inda matar da ta yi masa tambayar ta fito ba.
“Ban san daga wace jiha tambayar ta fito ba kuma ban ambaci sunan wata jiha ba, ballantana wasu suce da su nake wannan maganar.” Ya bayyana hakan ne a yayin da jaridar BBC ta tuntube shi ta wayar tarho,