LABARUN CIKIN GIDA NIGERIA

Hamza Al-Mustapha ya zargi wasu shugabannin Najeriya da zama silar lalacewar kasa – Tsohon shugaban tsaron bai lissafo sunayen shugabannin da suke da wannan alhakin ba

A cewarsa, matasan Najeriya suna da damar da za su samar da zaman lafiya a Najeriya Hamza Al-Mustapha, tsohon shugaban jami’an tsaro (CSO) lokacin mulkin janar Sani Abacha ya zargi wasu shugabannin Najeriya da lalata kasar.

Ya ce wasu shugabannin suna da burin gurbata kasa. Tsohon jami’in sojin ya sanar da hakan a wani taro da wata kungiyar matasa ta ciyar da Najeriya gaba ta shirya, kamar yadda TheNation ta ruwaito.

Al-Mustapha ya ce: “Wasu daga cikin shugabannin Najeriya basu da burin ciyar da kasa gaba, suna sanya hannu don a cutar da kasa.

Akwai abubuwan da Ubangiji ya boye wadanda har yanzu basu sani ba.

Al-Mustapha Abacha ya fallasa shirin wasu shugabanni na tarwatsa Najeriya.

A cewarsa, idan matasa suka hada kawunansu za su iya kawo karshen makiya. Ya kuma yi nuni a kan yadda za a samar da shugabanci mai inganci a kasar nan.

Sai dai ana cikin wannan batun, kasa ta rikice a kan wanda za a tsayar don ya gaji Buhari, an kara samar da wata kungiya wacce za ta tsayar da shugaban kasa na gaba.

Kungiyar arewa ta PDM, ta bayyana hakan a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, inda tace an kirkiri kungiyar don zabar shugaban kasa na gaba. Shugaban kungiyar Muhammad Auwal Musa, ya ce arewa ta gaji da zama tsakiyar talauci da ta’addanci a kasar nan.

A wani labari na daban, NAS ta bukaci shugaban kasa da yayi gaggawar sauke shugabannin tsaro a kan kashe manoman shinkafa 43 da ‘yan Boko Haram suka yi a Zabarmari, a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno,

jaridar Vanguard ta wallafa. Mr. Abiola Owoaje, wani jagaban NAS, ya gabatar da wata takarda mai taken “Kisan da ‘yan ta’adda suka yi na manoman shinkafan Zabarmari guda 43”, ya bayyana al’amarin a matsayin abu mai razanarwa da tsoratarwa.