Labaran Yammacin Yau
Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
An kama wasu ‘Yansanda da laifin karbar kudi da cin zarafin wasu mutane a Ribas.
Wasu ’yan kungiyar asiri sun fille kan wani Babban DPO Mai Kula da yankin Ahoada da da ke Karamar Hukumar Ahoada ta Jihar Ribas.
Za a tafka mamakon ruwan sama a Kano, Sakkwato da wasu Jihohi 20.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta haramta duk wani nau’i na kilisa da hawan angonci da taron majalisi ba tare da izini ba.
Wata mata ta kona Ɗanta da ruwan zafi a anguwar Hausawa dake Kalaba jihar Ribas kan zargin neman mata.
Wasu ‘yan bindiga sun harbe mutum 3 har lahira a ƙauyen Ugba da ke ƙaramar hukumar Logo a jihar Benuwai.
Kotu ta bai wa Abubakar Kusada kujerar majalisar wakilai a Katsina.
Kotu ta bai wa tsohon Gwamnan Binuwai Suswan nasarar zaɓen sanata.
Ana zargin wani ango ɗan shekara 21 da kashe matarsa a jihar Edo amma ya musanta zargin.
Kusan mutum 300 ne suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasa a kasar Moroko.
Rundunar sojan Mali ta sake fuskantar hare-hare a sansanoninta kwana ɗaya bayan masu iƙirarin jihadi sun kashe fiye da mutum 60.
Ukraine ta yi watsi da zaɓen da Rasha ta shirya a yankunanta.
Shinkafa ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 15 a Indiya.
Masu fafutuka za su maka Najeriya a kotu kan yanke wa Nijar wuta.
Burkina Faso ta kame wasu sojoji 3 da ke yunkurin kifar da gwamnatin Traore.