Labaran Yammacin Lahadi 19/11/2023CE – 05/05/1445AH
Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Shugaba Tinubu, yace a mulkinsa, babu ɗalibin da zai bar makaranta bai kammala ba saboda kawai ba zai iya biyan kudin makaranta ba.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Gwamnan Filato Muftwang, ta bai wa APC.
NDLEA ta kama wani gawurtaccen mai safarar miyagun kwayoyi wanda ya taba tserewa daga gidan yarin Kuje.
Sojojin Najeriya sun kama litar gas fiye da 15,000 na sata a Ondo.
An yi wa mata 61 aikin ciwon yoyon fitsari kyauta a jihar Gombe.
‘Yan sanda sun kama ‘ƙwararren ɓarawon akuya’ a Kaduna.
Gobara ta yashi a Gidan Shehu Shagari tsohon Shugaban Kasar Najeriya dake Sokoto.
Ƴan bindiga sun halaka babban fasto a jihar Kaduna.
Rundunar sojin Mali ta ce ta gano makeken ƙabarin da ‘yan tawaye suka binne mutane.
Kungiyar kare ‘Yan Jaridu ta (CPJ) ta yi kira da a sako ‘yan jaridu a Togo.
‘Yan gudun hijirar Rohingya sama da 500 sun isa Indonesia.
Mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra’ila.
Taiwan ta ce jiragen China takwas sun ƙetara iyakarta.
Ukraine ta ce Rasha ta ci gaba da yin luguden wuta a Kyiv.
Isra’ila a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa mayakan Houthi sun kwace wani babban jirgin ruwa na daukar kaya.
An ji karar jiniyar gama-gari a birane da dama na Isra’ila da ke kusa da iyakar Lebanon a ranar Lahadi a daidai lokacin da kungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila ke harba wa juna rokoki.