Labaran Yammacin Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da inga masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.

Shugaba Buhari yace yana kan bakan sa wajen ganin anyi zabe mai inganci a 2023.

Sojojin Najeriya sun ceto ‘yan China bakwai daga hannun ‘yan fashi.

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun bankawa ginin babbar Kotun jihar Imo wuta a Asabar ɗin nan.

Sabbin Takardun Kudin Da CBN Ya Fitar Sun Kare Tatas A Bankuna.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan Boko Haram 6 A Borno.

’Yan sanda a Jihar Kuros Riba sun tono gawar wakin wasu mutum 5 da aka kashe bisa zarginsu da maita.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya isa Owerri, babban birnin Jihar Imo don gudanar da taron yakin neman zabensa.

Tarayyar Afirka na kokarin soke takardar visa a tsakanin kasashen nahiyar.

Mutum 160 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Al’ummar kasar Tunisia na zaben ‘yan mjalisa a yau, yayin da jam’iyyun ‘yan adawa suka kauracewa zaben.

Putin ya tattauna da kwamndojin Rasha kan yakin Ukraine.

An rufe makarantu a China saboda korona.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da matakin Twitter.

Kocin Faransa Deschamps yace basu damu ba don mutane na son Messi ya ci Kofin Duniya.

Dan wasan tsakiyar Sfaniya da Barcelona Sergio Busquets ya sanar da cewa ya yi ritaya daga buga wa kasarsa kwallo.

Croatia ta doke Maroko da ci 2:1 a wasan neman mataki na 3 a gasar Cin Kofin.