Labaran Safiyar Yau

Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Shugaba Tinubu ya nada shugaban ma’aikatan jihar Lagas, a matsayin babban sakataren sa, ya kuma nada wasu hadimai na musamman guda 15, wadanda suka hada da Tanko Yakasai.
Shugaba Tinubu zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a yau.
Majalisar Dattawa ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake ta yaɗawa cewa ana ƙulle-ƙullen tsige Sanata Godswill Akpabio daga kan kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.
Gwamnan jihar Osun da wasu mutane sun tsallake rijiya da baya bayan wani abu ya fashe acikin jirgin Bombadier Global Express 6000 a Legas.
Shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya sha alwashin lashe zabe a jihar Imo.
Basarake Oluwo na Iwo yace abinda Obasanjo ya yi wa sarakuna a jihar Oyo a matsayin wulakanta masarautun gargajiya na Yarbawa basaraken ya nuna bacin ransa ga Obasanjo kan umartar sarakunan gargajiya a jihar Oyo da su tashi su gaishe da shi da Gwamna Seyi Makinde.
Allah Ya yi wa Ciroman Dukku rasuwa a Gombe.
An yi zanga-zangar kyamar Faransa a Vienna kan haramta sanya abaya.
Shugabannin kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar kulla kawancen tsaro da tattalin arziki a tsakaninsu.
Gwamnatin Birtaniya ta bayyana karin kudin bizar dalibai da ta masu yawon bude ido.
Wasu Yan Najeriya da suka makale a Sudan sunce suna cikin mawuyacin hali sakamakon yakin da akeyi a kasar.
Barcelona na son daukar dan wasan Manchester United Jadon Sancho, lokacin da alakarsa da Old Trafford ke kara tsami.
Cristiano Ronaldo zai maka tsohuwar kungiyarsa Juventus kotu kan sauran kudinsa fan miliyan 17 da ba a biya shi ba a lokacin korona.
Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Real Betis da ci 5:0 a wasan jiya.
Laliga: Valencia ta sami nasara akan Atletico Madrid da ci 3:0 a wasan jiya.
Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Ac Milan da ci 5:1 a wasan jiya.