LABARAN SAFIYAR YAU
Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Shugaba Tinubu ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe za ta yanke domin yana da yakini shi ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023, a cewar fadarsa.
Gwamnatin shugaba Tinubu zata binciki yadda aka yi da kudin shirin samar da abinci na Anchor Borrowers.
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun fara yajin aikin gargadi.
Jami’an ‘yan sandan jihar Edo sun cafke mai shekara 31 bisa zargin aikawa manemin auren tsohuwar budurwarsa hotunanta tsirara.
‘Yan sandan Filato sun kama mace da zargin satar jaririya.
‘Yan sandan Filato sun kama tsoho mai shekaru 63 John Mahanan bisa laifin yi wa yara kanana masu shekaru 4 zuwa 8 fyade a kauyen Mabel dake karamar hukumar Butura.
Gwamnatin Kaduna ta samar da motoci guda 5 da za a rika amfani da bin marasa lafiya har gida domin basu kulawa yadda ya kamata.
Gwamna Zulum ya ƙaddamar da shirin shuka bishiya miliyan ɗaya.
Magidantan da ’yan bindiga suka kashe a Masallaci a Kaduna sun bar marayu 61.
Masana sunce rashin cunkoso a titunan Legas asara ce ga Najeriya.
Sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane 6 a Filato.
Gwamnan jihar Delta ya naɗa ɗan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata, a matsayin mashawarci na musamman.
Jami’n tsaron Isra’ila sun raunata Falasɗinawa biyar a Jenin.
Kaso 70 na daurarrun gidajen yarin Ghana matasa ne.
Congo ta cafke manyan sojojinta bayan mutuwar mutane 50.
Amnesty International ta ce sojojin Eritiriya sun aikata laifukan yaki a Tigray.
Wasu jami’ai daga Saudiyya sun isa Ingila, don gwada sa’ar ƙarshe a ƙoƙarinsu na shawo kan Liverpool ta amince ta sayar da Mohamed Salah a kan fam miliyan 200 kafin ranar Alhamis.
Jadon Sancho, zai iya rasa madafa a Mancheter United a wannan kaka, sai dai fa idan ya kufce ya tafi Saudiyya, a cewar, Rio Ferdinand.
Manchester United na ƙoƙarin ganin ta sayar da Eric Bailly da Donny van de Beek, kafin a rufe kasuwar hada-hadar ‘yan wasa ta ƙasar Saudiyya ranar Alhamis.