LABARAN SAFIYAR YAU
Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin masana’antu ta G-20.
Gwamnatin Najeriya tana nazarin shiga ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin duniya, ake yi laƙabi da G-20.
Kotu ta sallami matar da ta haihu a Gidan Yari a jihar Ekiti.
Mutum 3 sun mutu bayan faduwar Wani bene da ake aikin gininsa, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.
Wasu ‘Yan Bindiga sun bude wuta a kan titi, sun yi awon gaba da mutane a Abuja zuwa Lokoja.
Majalisar Dokokin Gombe ta ki tantance mutum 17 da Gwamnan jihar ya aike mata don nadawa Kwamishinoni kwanaki 38 da suka gabata.
NNPP za ta yi bincike a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan 1 da aka samu daga sayen fam.
Lauretta Onochie wanda ta yi aiki da Muhammadu Buhari ta samu kan ta a cikin matsalar matsuguni a kasar Birtaniya.
Gwamnatin jihar Rivers ta garkame gidan talabijin din AIT da gidan rediyon RayPower.
Mummunar guguwa ta afka wa Taiwan.
‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga bayan yunƙurin ƙona Al Qur’ani a Sweden.
Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Osasuna da ci 2:1 a wasan jiya.
Seria A: Juventus ta sami nasara akan Empoli da ci 2:0 a wasan jiya.
Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Fiorentina da ci 4:0 a wasan jiya.
Lig 1: PSG ta sami nasara akan Lyon da ci 4:1 a wasan jiya.