Labaran Safiyar Litinin 25/12/2023 CE – 11/06/1445AH

Labaran Safiyar Litinin 25/12/2023 CE – 11/06/1445AH

Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da aka kai ƙauyen Mushu da ke karamar hukumar Bokkos Jihar Filato.

’Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen wayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.

An karkatar da Naira bilyan 37,170,855,753 zuwa asusun wani ‘dan kwangila, shi kuma ya cire kudin ya sayi motoci da gidaje a Abuja da Enugu a tsohuwar Gwamnatin shugaba Buhari daga Ma’aikatar jinkai.

Toshon Gwamnan CBN yayi karar wadanda suka fitar da cewar ya mallaki asusun ajiya na kasashen ketare har 593 ya kuma musanta hakan

NDLEA ta kama uwa da ɗanta kan safarar kwayoyi a Legas.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 11 a yankin Achimbi da Gumanyi da ke unguwar Kwaku a yankin Kuje a Abuja.

Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya musanta zargin da ake yi masa na tafka barna a lokacin da yake rike da babban banki kasa na CBN.

Fasinja 1 ya rasu yayin da wani ya samu rauni bayan da wata motar bas ta yi hatsari a yankin Abaji da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Ana ci gaba da zanga-zanga a Serbia don neman a je zagaye na biyu na zaɓe.

Hukumar zaɓen Kongo ta yi watsi da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar.

Masar ta gabatar da wani tayin matakai uku don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

‘Yan kasar Chadi sun jefa kuri’ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Mutane 13 sun rasa rayukansu a wata fashewar da aka samu a Indonesia.

Isra’ila: Natenyahu ya tabbatar da tafka hasarar rayukan Yahudawa masu yawa a yakin da suke da Hamas.