Kwankwaso: Ya Gara takan yi da Dutse?
Siyasar Arewa tin lokacin dauri ta gaji yarfe da kazafi da yada karya har ta zama jiki a salon adawa da karya abokin hamayya, abin ya kara muni cikin 1983 saboda misayan zafafan kalamai da farmaki ga juna tsakanin tabo da santsi wanda ya jawo asarar rayuka da muggan raunuka da lalacewar zumunci hadda rabuwar aure.
Wato idan Dan siyasa ya samu karbuwa ko aka fuskanci jam”iyyarsa ta shiga ran talakawa to sai gobarar hamayya ta kama ganga-ganga, wani a jefe shi da sha’awar jinsi, kai da sanin shugaba wane ake tayar da kayar baya, ku guji jam’iyyar mai cross, wane fa ya goyi bayan batanci ga Ma’aiki (SAW) kuma mun sami labarin yana tare da masu zagin sahabbai, kai yan kogo suna tare da shi dan zai sako malaminsu.
Du zabe na zuwa da hakan kuma yana wucewa wani loton yakan tasiri, amma a mafi yawan lokaci yana bin ruruma sai dai tashin zance, kawai abin mamakin cikin 2023 yadda wasu yan uwa masu da’awa suka fara ruduwa da irin wannan jita-jita har suke bijiro da tambaya a shafinsu, wasu sun dauki matsaya tinda yan kogo na cewa za su yi zabe bana amma ana tinanin su dauki jam’iyyar Adawa,
Kai da Kur’ani ya koya maka idan fasiki ya zo da labari ka bincika? Suratul Hujrat ta ja kunnenka kan zargi mara tushe, Hadisin Tirmizy na Abu Huraira ya lissafo maka abu 8 da dole du musulmi ya kula kan musulmi zaka bi rudin social media? Umar Bn Khaddab (RA) ya ce tinda wahayi ya yanke yanzu ba mu iya sanin mai ke zuciyar mutane don haka mukan yi hukunci da abin da ya bayyana, idan Alheri ya bayyana daga mutum sai mu kusanto da shi mu amince masa, idan muka lura da kishiyar hakan ba maganar aminci ko gasgata ko waye, don Allah wannan ma’auni da Bukhary ya rawaito bai isa ba?
Ina Godiya ga Allah tin 1997 nai Tawayiya don yaki da masu zagin sahabbai, na je har filin Babban Dodo tare da Malam sunusi jibril jega don raddi ga Angon simbiyatu; shi kuwa Audu Nasiru mun yaki shubuharsa gwargwadon iko to wacce siyasar ce zata sanya shakka kuma a babi mafi girma Tauhidi ? Ashe kokwanto na kau da yakini? Muna iya rungumar Maslaha mutawahhama mu yi wurgi da mutahakka a ilmin kawa”id kenan? Lallai yan uwa ku lura da siyasar kano cikin yan kwanakin nan, wai kun san wani Dan jarida ya rubuta karya kan Deborah ya ce kwankwaso ne ya fada? Kuma ya zo ya karyata kansa!
One of the great secrets of success is for you not to worry about things that you can’t do anything about, wannan shi ke taimakon Rabiu kwankwaso a hakika tinda ba yadda za a hana irin wannan jita-jita yaduwa, amma na karanta cikin sunan idan ruwa ya kai matsayin Tulu biyu baya daukar najasa to kuwa babu yadda karya zata rushe gaskiya, du kokarin mai Buhutani zai gajiya masu haske cikin zukata kuma za su fahimci inda gizo yake sakar.
Ibrahim Mu’azzam Senator
Ibrahimmuazzam38@gmail.com