Kungiyoyin Kwadago na kasa NLC da TUC zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar 3-October-2023
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ba da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba a fadin kasar.
Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka kira da yammacin ranar Talata a babban birnin kasar, Abuja.
Sun bukaci rassansu na jihohi su harhado kan ‘yan kwadago da sauran jama’a don gudanar da jerin zanga-zanga da maci a fadin Najeriya.
Kafofin labarai a Najeriya na cewa sun fahimci cewa shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu sun warware bambance-bambancen da suka sanya kungiyar NLC shiga wani yajin aikin gargadi tsawon kwana biyu, ba tare da takwararsu ta TUC ba.
NLC ta kaurace wa aiki a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Satumba da muke ciki don matsa lamba ga gwamnatin kasar a kan ta shawo kan wahalhalun da ‘yan Najeriya, musamman ma’aikata ke ciki, sakamakon cire tallafin man fetur.
A cewar sanarwar da sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja ya fitar, kungiyoyin na gudanar da taron ne ta intanet.
A lokaci guda kuma, ministan kwadago, Mista Simon Lalong ya roki shugabannin NLC su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati na nan a kan kudurin magance damuwar da suka bijiro da ita.
Ministan – kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito – ya kuma nunar da cewa daya daga cikin manyan bukatun NLC a taron da suka yi na baya, tuni an cimma ta, inda ta ba da umarnin sakin shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota a kasarnan