Kungiyar NLC na neman Gwamnan Kaduna ruwa a jallo: Yajin aikin ‘yan kwadago:

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta bayyana cewa tana neman gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ruwa a jallo, kana duk wanda ya gan shi, ya kama shi zai samu tukuici mai gwaɓi.

Sanarwar kungiyar na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan shima gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yana neman shugaban kungiyar kwadago ta Najeriyar Ayuba Waba ruwa a jallo, da shi da sauran jagororin kungiyar.

Ana wannan tataburza ne yayin da kungiyar ke ci gaba da gudanar da yajin aiki da zanga zanga a jihar ta Kaduna, inda gwamnati ta sallami dumbin ma’aikata a baya bayan nan.

Mai magana da yawun kungiyar kwadago ta Najeriyar Kwamaret Nasir Kabir, ya shaidawa BBC cewa sun kuma yanke shawarar fara yajin aiki na kasa baki daya daga ranar litinin, saboda yadda aka kai ‘yan daba da zummar tarwatsa zanga zangar da suka gudanar a ranar Talata.

Ya ce lamarin ya sa kungiyar gudanar da wani taron gaggawa, inda suna cikin taron ne suka samu labarin cewa gwamnan jihar ya sauyawa shugaban kungyarsu a jihar wurin aiki zuwa Birnin Gwari, inda ake fama da matsalar tsaro.

”A wannan taron ne kuma muka samu labarin cewa ya sallami dukkanin ma’aikatan lafiya ‘yan kasa da matakin albashi na 14, da kuma maganar da ya yi wa ‘yan jarida ta cewa yana neman mu” inji mai magana da yawun kungiyar ta NLC.

A cewarsa muna ”muna kira ga dukkan jama’a da kuma jami’an tsaro su ba mu rahoto da zarar sun ga El-Rufa’i a duk inda suka ganshi, sannan mun bukaci jami’an tsaro su kamo shi domin ya fuskanci hukunci shari’a saboda matakin da ya dauka na sallamar ma’aikata ba bisa ka’ida ba” inji Kwamared Nasir.

A halin da ake ciki dai tuni aka soma yin kira ga dukkanin bangarorin biyu su yayyafawa zukata ruwa don warware matsalar cikin ruwan sanyi.

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC na cikin masu irin wannan kira, inda shugabanta gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya yi kira ga gwamnan na Kaduna ya zauna da ‘yan kwadagon a teburin sulhu.

NLC ta shaidawa BBC cewa a halin da ake ciki shugabanta na kasa Ayuba Waba wanda kuma shine shugaban kungiyar hadin kan ‘yan kasuwa ta duniya ITUC, da gwamna El-Rufai ya yi barazanar kamawa, na wata ganawa da shugabannin kungiyar na kasashen duniya kan halin da ake ciki a Najeriya.

Tuni dai itama kungiyar ,a’aikatan man fetur da iskar gas ta duniya ta Najeriya wato NUPENG ta yi barazanar tsayar da al’amuran man futur da iskar gas cik a Najeriya, dangane da abun da ta kira ”musgunawa jama’a” da ya saba yi ba.