Ku Dinga Fadin Gaskiya Ga Masu Mulki, Buni Ya Gayawa Malaman Addini

Ku Dinga Fadin Gaskiya Ga Masu Mulki, Buni Ya Gayawa Malaman Addini

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bukaci malaman addini da su rika fadin gaskiya ga masu mulki ba tare da la’akari da alakarsu da shugabannin siyasa ba.

Gwamna Buni ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta yini daya da manyan limamai da masu wa’azin addinin musulunci na kananan hukumomi 17 na jihar gabanin fara tafsirin Alkur’ani a watan Ramadan.

Gwamnan wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta ya ce: ‘’Ya kamata ku yi mana wa’azi ku gaya mana gaskiya domin mu cika alkawuran da muka dauka.

”Kada ku ji tsoron fadin gaskiya. Ku ci gaba da tunatar da mu cewa dukanmu za mu mutu kuma mu bayyana a gaban Allah wata rana don yin lissafin aikinmu. Wadannan za su canza tunaninmu daga dabi’ar sata da rashin gudanar da mulki.’’

A halin da ake ciki, Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya bukaci malaman addinin Musulunci da su jagoranci mabiyansu wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin tafsirin watan Ramadan da kungiyar Jama’atu Izalatul Bidiah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta gudanar a Katsina a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnan ya jaddada muhimmancin addu’o’i wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman kan harkokin addini (Izala), Malam Gambo Dan’Agaji, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafa wa ayyukan addini saboda muhimmancin da suke da shi a harkokin ruhi da na duniya.

Shugaban taron, Alhaji Muhammad Usman Sarki, ya yi nuni da kalubale iri-iri da suka hada da rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da jihar ke fuskanta, inda ya jaddada cewa Allah ta hanyar yin addu’o’i na da matukar muhimmanci wajen rage radadin da jama’a ke ciki.