Kotunan Najeriya za su fara gudanar shari’a ta intanet
Ma’aikatar shari’ar ta Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon tsari da zai bai wa kotuna damar sauraron shari’o’i daga nesa ta hanyar amfani da intanet.
Gwamnatin ƙasar ta ce tsarin zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen yari, da kuma kare waɗanda ake tsare da su, har ma da jami’an tsaron gidajen yari daga fada wa hannun miyagun mutane da kuma saboda annobar korona.
Abubakar Malami,wanda shi ne ministan shari’a na Najeriya ne ya kaddamar da wannan sabon tsarin, inda aka far misali da gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja babban birnin kasar.
Dakta Umar Jibrilu Gwandu, shi ne mai taimaka wa ministan kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ya ce wannan tsarin zai kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i a fadin kasar da zarar an kaddamar da shi.
“Wannan somin tabi ne, kuma yana da manufar kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’a, da kuma rage cunkoso a gidajen yari.”
Ya kara da cewa tsarin zai rage yawan zirga-zirgar da ake yi da wadanda ake tuhuma da aikata laifuka daga gidajen yari zuwa kotuna, ciki har da wadanda ke wakiltarsu wato lauyoyi da sauran ma’aikata kamar gandirebobi.
Shin wannan shirin bai taka kundin tsarin mulki ba?
Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya ce wannan sabon tsarin ya yi daidai da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya: “Sashe na 36, karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce a saurari dukkan shari’o’o a bainar jama’a ba tare da boye-boye ba.”
Su ma ma’abota shari’a sun yaa da wannan sabon matakin na ma’aikatar shari’a.
Barista Aisha Isa wata lauya ce kuma tana cikin ‘ya’yan kungiyar lauyoyi da ke aikinta a jihar Yobe ta Najeriya.
“A yadda aka saba, a duk lokacin da muke son a gabatar da wani a gaban shari’a, sai mun aika da sammaci muna bukatar yin hakan. Wata ran mu kan fuskanci matsaloli kamar na rashin abin hawan da za a dauko wanda ake tuhuma, ko matsalar jinkirin aikawa da sammacin da sauran su.”
Ta ce wannan tsarin zai kawar da dukkan wadannan matsalolin domin ta intanet za a haska kowa, kuma babu dalilin da za a samu jinkiri kamar a baya.