Kotun koli ta haramtawa gwamnatin Najeriya sakin kason kudaden kananan hukumomin da ba a yi zabe ba

Kotun koli ta haramtawa gwamnatin Najeriya sakin kason kudaden kananan hukumomin da ba a yi zabe ba

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kotun kolin kasar ta haramta wa gwamnatin tarayya sakin kason kudade ga kananan hukumomin da ba a yi zabe ba da gwamnan jihar ya nada.

Kotun kolin ta bayar da wannan umarni ne a lokacin da take yanke hukunci a kan kararrakin cin gashin kan kananan hukumomi da babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar a madadin gwamnatin Najeriya.

A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Emmanuel Agim ya haramtawa Gwamnatin Tarayya ci gaba da biyan kudaden kason LG ta hannun gwamnatocin Jihohi, inda ya yi nuni da cewa gwamnonin sun ci zarafinsu.

Mai shari’a Agim ya zargi gwamnonin jahohin da rike kason kudaden da suke amfani da su yadda suka ga dama, wanda hakan ke cutar da kananan hukumomin.