Kotu ta yanke wa wasu ‘yan banga 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa wasu ‘yan banga 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta yanke wa wasu ‘yan banga biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wani matashi mai suna Ahmad Musa (Khalifa) dan shekara 17 a Sabon Titin Panshekara na jihar Kano.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Emmanuel Korau, Eliesha Ayuba Jarmai, Irimiya Timothy, Auwalu Jafar da Mustapha Haladu.

An same su da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma kisan kai wanda ya ci karo da sashe na 97 da 221(b) na dokar Penal Code.

Wadanda aka yankewa hukuncin dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.

Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu biyar don tabbatar da tuhumar da ake musu.

Lauyan da ake kara, Barista Ahmad Muhammad, ya gabatar da shaidu shida ciki har da wadanda ake kara.

Sai dai babban alkalin ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da shari’ar ba tare da wata shakka ba, don haka ta yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin da ya dace.

Lauyan mai shigar da kara, Barista Lamido Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Junairu, 2022, wadanda aka yanke wa hukuncin, wadanda ‘yan kungiyar ’yan banga ne da ke cibiyar matasa ta Sani Abacha, suka hada baki tare da kaiwa marigayi Ahmad Musa hari, a Sabon Titi.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi amfani da wata doguwar sanda (gora) inda suka yi wa mamacin duka da shi, sannan wanda ake kara na farko ya yi amfani da wuka ya daba wa marigayin a wuya.

Daga baya ne suka dauki gawar marigayin a cikin babur uku zuwa ofishinsu.

Daga baya an kai marigayin zuwa sashin ‘yan sanda na Kuntau inda aka garzaya da shi asibiti.

Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.