Kotu ta hana Aminu da wasu mutane 4 kiran kansu Sarakuna har abada

Kotu ta hana Aminu da wasu mutane 4 kiran kansu Sarakuna har abada

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 17, karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta dakatar da Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tsige daga sarautar Bichi, da Rano, da Gaya, da kuma Karaye a matsayin sarakuna har abada.

Da take zartar da hukuncin a ranar Litinin, kotun ta kara dagewa Sarkin Kano na 15 da wasu sarakuna hudu, su kansu, hadimai, masu zaman kansu da duk wani mutum da suka nada daga bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano, Karaye.

Gwamnatin jihar Kano dai ta shigar da kara ne inda ta bukaci Mai Martaba Sarkin Kano da ya dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da wasu sarakunan Karaye da Bichi da Rano da kuma Gaya hudu daga gabatar da kansu a matsayin sarakuna.

Gwamnatin ta kuma baiwa Sarakunan da aka tsige sa’o’i 48 da su fice daga fadarsu bayan an sauke su.

Cikakkun bayanai mai zo daga baya…