Kotu ta daure Sadiya Haruna wata shida
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a kan fitacciyar mai sayar da kayan mata, Sadiya Haruna a bisa laifin batanci ga wani darekta a harkar fina-finai, Isa I. Isa.

Kotun ta majistare wadda ke zama a filin jirgin sama na mallam Aminu Kano, ta same ta da laifin batanci ga darektan wanda ya kai ta kara, a shafinta na Istagram, a yau Litinin 07 ga watan Fabrairun 2022.
Kotun ta kuma zartar da cewa kada wadda aka samu da laifin ta kara wani rabutu ko sanya wani abu a wani shafinta na sada zumunta da muhawara, wanda zai zama na batanci ga wani nan da shekara daya, idan ba haka ba za a sake yanke mata wani hukuncin na shekara biyu.
Sai dai kuma Sadiya Harunar tana da damar daukaka kara kan hukuncin kotun.