Kotu ta amince da zaben bangaren Ibrahim Shekarau a Kano
Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta amince da zaben shugabannin Jam’iyyar APC na Jihar Kano bangaren Malam Ibrahim Shekarau wanda ke karkashin jagorancin Alhaji Haruna Ahmadu Danzago, yayin da tayi watsi da bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Alkalin Kotun Tarayyar dake Abuja Hamza Mu’azu ya yanke hukuncin amincewa da bangaren tsohon gwamnan sakamakon karar da ya shigar inda yake kalubalantar halarcin bangaren gwamnan mai ci wanda aka zabi Alhaji Abdullahi Abbas.
Wannan ya biyo bayan tarurrukan jam’iyyar guda biyu da akayi a birnin Kano a ranar 16 ga watan Oktoba wanda Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Shekarau suka jagoranta a wurare daban daban.
Kwamitin kula da kararrakin zabe na Jam’iyyar APC ya amince da bangaren Gwamna Ganduje wanda aka zabi Abdullahi Abbas, yayin da bangaren Malam Shekarau ya ruga kotu domin neman hakkkin su.
Rikicin cikin gida na nema jefa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya cikin mummunar yanayi a daidai lokacin da ake tinkarar zaben shekarar 2023.
Rahotanni sun ce lokacin gudanar da taron Jam’iyyar da akayi a jihohin kasar 36 an samu rarrabuwar kawuna a jihohi da dama cikin su harda jihar Kano da Lagos inda aka gudanar da tarurruka bibbiyu da kuma samun shugabanni bibbiyu a jihohin wadanda ke da matukar tasiri ga jam’iyyar.
Wannan na daga cikin matsalolin da suka hana Jam’iyyar gudanar da taron ta na kasa domin zabo shugabannin da zasu jagorance ta a matakin kasa.
Ko a makon jiya, shugaban jam’iyyar na riko Mai Mala Buni da shugaban gwamnonin APC Atiku Bagudu da Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da halin da jam’iyyar ke ciki da kuma shirin taron ta na kasa, inda suka yanke hukuncin sanya watan Fabarairu mai zuwa a matsayin lokacin taron.
Gwamna Bagudu yace za suyi amfani da lokacin da suke da shi kafin watan Fabarariru domin warware matsalolin cikin gidan da suka shafi zaben jihohin da ake rikici akan su.