Kotu a Abuja ta yanke wa ɓarawon jaka hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru 4
Kotun Grade 1 dake unguwar Kubwa Abuja ta yanke wa wani mahauci mai suna Bilia Zakari mai shekara 20 hukuncin ɗaurin shekaru 4 a gidan kaso bayan ta kama shi da laifin fizge wa wata mata jaka a Abuja.
‘Yan sandan da suka kama Zakari sun kai shi kara kan kotu ne kan laifin yin kwace ta karfi da tsiya, ji wa matar da yayi wa kwace rauni da sata.
Alkalin kotun Muhammad Adamu wanda ya yi watsi da rokon sassaucin da Zakari ya yi ya ce ya yanke wannan hukunci haka ne domin ya zama ishara ga masu yi wa mutane kwace a Abuja.
Lauyan da ya shigar da kara Babajide Olanipekun ya bayyana wa kotu cewa Awele Ruth ta kai karar Zakari ofishin ‘yan sanda dake Gwagwa ranar 2 ga watan Fabrairu.
“Ruth ta ce a wannan rana Zakari ya yi kokarin kwace mata jaka a hanyar zuwa wurin aiki.
“Ruth ta ce Zakari ya kwace mata waya da wasu kayan ta masu daraja.