X

Kimanin makonni biyu bayan yi wa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na jihar Taraba Jolly Nyame ahuwa

Hankali ya karkata kan tasirin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, da kuma rawar da gwamnati ke takawa a yunkurin yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya.

Ranar Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na jihar Taraba Jolly Nyame ahuwa, wadanda da farko kotu ta yanke ma su hukumcin daurin shekaru 14 kowannen su a shekara ta 2018, bayan da kotu ta same su da laifin badakalar kuli da jimilar su ta kai Naira biliyan 2.22 tsakaninsu.

Gwamnatin Buhari ta yi wa tsofaffin gwamnonin ne ahuwa tare da wadansu fursunoni 159 bisa dalilai dabam dabam da suka hada da dalilan jinkai da kuma rashin lafiya.

Tsofaffin gwamnonin sun yi mulki daga shekara ta 1999 zuwa 2007. Da farko, wata kotu da ke zama a Abuja ta yankewa Dariye hukumcin daurin shekaru 14 amma kotun daukaka kara ta rage wa’adin zama gidan yarin zuwa shekaru 12, yayinda kotun kolin kasar ta goyi bayan hukuncin bayanda tsohon gwamnan Dariye ya daukaka kara. Kotun kolin ta kuma goyi bayan hukumcin daurin shekaru 12 da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame.

Kwanaki biyu bayan yiwa tsofaffin gwamnonin ahuwa, wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan harkokin mulki da al’amuran yau da kullum a Najeriya da ake kira Kungiyar fafatukar kare hakin ‘yan kasa da tabbatar da shugabancin kwarai da ake kira “the Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP)” ta shigar da kara tana kalubalantar yiwa tsofaffin gwamnonin ahuwa.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sake shawara ba tare da bata lokaci ba, ta janye afuwar da ta yi wa tsofaffin gwamnonin, yayinda kungiyar ta yi barazanar maka gwamnatin a kotu idan ba ta janye ba.

Tun sanar da yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa dai, ake ta tafka mahawara a ciki da wajen Najeriya. Lamarin da ake alakantawa da siyasa.

A hirar ta da Muryar Amurka, Naja’atu Mohammed wata mai kula da lamura a Najerya ta bayyana cewa, gwamnatin ta dauki wannan matakin ne da wata manufa da ba ta fita ta bayyanawa ‘yan Najeriya ba. Bisa ga cewarta, idan gwamnatin Buhari ta yafewa tsofaffin gwamnonin, ai ‘yan Najeriya da suka cuta ba su yafe ba sabili da haka bai kamata a sake su ba.

Shi ma a nashi tsokacin, shugaban kungiyar da ke sa ido kan harkokin mulki da neman ganin an yi adalci, Auwal Musa Rafsanjanni ya bayyana cewa, yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa maida hannun agogo baya ne a yaki da cin hanci da rashawa. Ya bayyana cewa, doka da shari’a suna cin talakawa ne kawai ganin yadda manyan ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suke cin karen suba babbaka yayinda ake kuntatawa talakawa. Ya yi bayani da talakan da ya saci kwalayen indomi da kudinshi bai wuce Naira dubu 25 ba, domin ya rasa hanyar ciyar da iyalinshi, amma duk da bayanin da kuma sha’awar da masu hali baiwa su ka nuna ta tallafa wa mutumin da ke fama da talauci, aka yanke ma shi hukumcin dauri a gidan yari.

Fitattun ‘yan Najeriya da suka kushe wa yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa sun hada da fitaccen lauya kuma dan fafatukar kare hakkin bil’adama Femi Falana da fitaccen marubuci da ya sami lambar yabo ta Nobel Wole Soyinka wadanda suka yi Allah wadai da matakin da su ka ce ya saba hankali.

A hirar shi da manema labarai jim kadan bayan sanar da afuwar, Farfesa Soyinka ya bayyana cewa, wannan na nufin yaki da cin hanci da rashawar da gwamnatin Buhari ta ce tana yi “ya kare.”

A nashi tsokacin, fittacen lauya mai kare hakkin bil’adama Femi Falana ya bayyana cewa, ana murde tsarin shari’a domin kyautatawa ‘yan siyasa da muzantawa talakawa. Ya bayyana Afuwar da fasa kwai a fuskar Najeriya da ya ce zai dauki lokaci kafin ‘yan Najeriya su manta.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings