Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Azpilicueta, Dembele, De Jong, Mee, Messi, Ibrahimovic

Lionel Messi, mai shekara 34, ya fara nuna damuwarsa kan ko kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino zai iya ciyar da kungiyar gaba saboda irin kamun ludayinsa da kuma rashin iya tsawata wa ‘yan wasan kungiyar. (L’Equipe, via Mirror)

Dan wasan baya na Chelsea kuma dan kasar Sifaniya Cesar Azpilicueta mai shekara 32 na tattaunawa da Barcelona gabanin komawarsa kungiyar a karshen wannan kakar wasan. (El Nacional, via Daily Mail)

Manchester Unitedta bi sahun Newcastle United wajen kokarin dauko dan wasan Barcelona Ousmane Dembele mai shekara 24 bayan da dan kasar Faransan ya bayyana cewa zai so ya sake kungiya. (Mundo Deportivo, via Express)

Kocin Newcastle Eddie Howe na shirin dauko Tyrese Campbell, dan wasan Stoke mai shekara 21 a matsayin dan wasa na farko da kungiyar za ta dauka tun bayan da kungiyar da ke wasanta a St James’ Park ta koma hannun ‘yan kasar Saudiyya. (Sun)

Sabon kocin Manchester United Ralf Rangnick na kwadayin dauko Frenkie de Jong dan wasa mai shekara 24 na Barcelona da kasar Holland yayin da yake kokarin sake gina kungiyar da ke wasanta a Old Trafford. (El Nacional, via Daily Star)

Chelsea ta kammala daukan Attila Szalai, dan wasan baya mai shekara 23 daga Fenerbache, kamar yadda mai gidansa na Hungary Marco Rossi ya bayyana. (Mirror)

Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic mai shekara 40 ya bayyana sha’awarsa ta ci gaba da buga tamaula a kungiyar mai wasanninta a Gasar Serie A ta Italiya har zuwa ranar da zai yi ritaya. (Star)

Dan wasan baya dan kasar Portugal Diogo Dalot mai shekara 22 ya sanar cewa ba zai bar Manchester United nan kusa ba, matakin da ya rufe kofar komawarsa wata kungiyar. (Daily Mail)