Kasar Masar Ta Buda Kan Iyakoki Ga ‘Yan Nijeriya
A karshe dai hukumomin Masar sun amince da baiwa ‘yan Najeriya da ke gudun hijira a makwabciyarta Sudan damar wucewa ta kasarta.
Sakamakon rufe sararin samaniyar kasar Sudan, gwamnatin tarayya ta yi tanadin motocin bas da za su kai ‘yan Najeriya zuwa Masar daga inda za su kama jiragen da ke komawa gida.
Sai dai ‘yan Najeriya sun makale a kan iyakar kasar Masar sakamakon kin amincewar kasar na ba da izinin wucewa duk da rokon da aka rika yi.
Sai dai da yammacin ranar Litinin din da ta gabata ne shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce kasar Masar ta amince ta bude kan iyakarta bayan shigar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ta ce shugaban na Najeriya ya tuntubi shugaba Abdel Fattah El-Sisi, takwaransa na Masar, kafin ya kai ga cimma matsaya.
Dabiri-Erewa, ta ce Masar ta amince da bude iyakar a karkashin wasu tsauraran sharudda.
“An bude iyakar, (tare da tsauraran sharudda) bayan da Shugaba Buhari ya shiga tsakani da Shugaban Masar. Don haka za a fara aikin jigilar mutanen da ofishin jakadancin Najeriya da ke Masar zai yi,” in ji Dabiri-Erewa a cikin wata sanarwa.
‘Yan Najeriya da suka tashi daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan a ranar Larabar da ta gabata, sun gamu da ajalinsu a kan iyakar Sudan da Masar kan wasu batutuwan da suka shafi biza.
Sama da daliban Najeriya dubu sun makale tsawon kwanaki a kan iyakar Masar.