“Kare Kayayyakinmu” INEC ta roki ‘yan Najeriya

Biyo bayan hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta a sassan kasar, a jiya hukumar zabe mai zaman kanta ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ga cewa ta…

Biyo bayan hare-haren da ake kai wa ofisoshinta a sassan kasar, a jiya hukumar zabe mai zaman kanta ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ga cibiyoyinta a matsayin kadarorin kasa da kuma kare su gabanin babban zabe na 2023.

Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan roko a wani taro da kungiyar dattawan Afrika ta yamma da aka gudanar a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Tawagar dai ta samu jagorancin tsohon shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma da tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Gambia Fatoumata Jallow-Tambajang.

Yakubu ya ce, “Akwai wasu guraren da ke damun su, babban wanda shi ne rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan. A cikin kasa da makonni biyu an kai hari a wasu ofisoshin kananan hukumominmu guda uku a fadin kasar, wanda ya kawo adadin hare-haren zuwa bakwai a cikin watanni hudu da suka gabata.

“Yayin da muke son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za mu murmure daga wadannan hare-hare, kuma zaben zai gudana kamar yadda aka tsara, muna son yin kira ga daukacin ‘yan kasar da su ga kayayyakin hukumar a matsayin kadarorin kasa.

“Hakinmu ne na hadin gwiwa mu hada karfi da karfe wajen kare su. Dole ne a daina kai hare-hare kuma a gaggauta cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su gaban kuliya.

“Dole ne in kara da cewa tare da shugabannin yankin da ake mutuntawa da suka hadu a matsayin dattawa don ingantaccen zabe, ina da yakinin cewa ba za a samu raguwar shiga tsakani a cikin rikice-rikice ba da kuma yawan ayyukan sa ido kan zabe a lokacin zaman lafiya.”

Tun da farko, Koroma, ya ce sun je Najeriya ne a wani shirin sasantawa kafin zaben, domin tunkarar matsalolin da suka shafi nasarar zabe a Najeriya da ma sauran sassan yankin.