Kano tana tangal-tangal

Daga: Ibrahim Mu’azzam Muhd.

Lokacin da jahohin kudu maso Yamma suka tsangwami Makiyaya Fulani har ta kai kowanne laifi ana jingiwa gare su, haka jahohin Benue da Pilato da Adamawa da Taraba suka kwaikwaya, Gwamnatin Tarayya ta zuba Ido har abin ya kazanta yakai ga asarar jini da Dukiya da sabbin Dokokin hana kiwo, sai daga karshe aka zo da maslaha ta RUGA kuma jahohin sukai tsalle suka ki aminta dole aka hakura.

Ni babban Tinanina a lokacin mai zai biyo bayan hana Bafulatani kiwo? Mawallafin Raudul Jinan Gidado B. Laima ya bayyana mana yadda Fulani suka amsa kiran Dan Fodiyo Don tsira daga Azzaluman sarakuna masu kwacen Mata da Shanaye, to yanzu da Fulanin Daji ke rayuwa ba Addini ba Karatu kiran wa za su amsa? Amsar nan a fili take indai kana bin Titinan Arewacin Nigeria a Yau.

To Yanzu dai kun ga Arewacin Nigeria ya doshi Gargara domin tini Kanuri suka dau makami da sunan Jahadi, suma Fulani sun fake da kare Kai sun zama yan fashin Daji da tare hanya da neman fansa, idan ka lura saura kabila daya Tal wato Hausawa masu cibiya a Kano, babu abin da ya kamata gare mu sai kokarin magance matsalar kabilun can biyu da kokarin dakile Yaran Hausawa daga dikkan wani tinanin Ta’addanci don kara tin yana danye ake Tankwara shi, Gwamnati ke zata shige gaba mu kuma mu dafa mata.

Kun ga abin da ke faruwa yanzu a Kano na Daba da Fizgen Waya kana da illata du abin da akai karo da shi a Hanya kar mu dauke shi da wasa, idan ka duba littafin The Kano Civil War and British over Rule 1822-1940 ibadan: OUP na Clapperton, H. zaka fahimci Kano Gari ne da sakaci ko wasarere Kan iya dagula masa lissafi, sai ya sa Tsayayyun Shugabanni suka fi yin Nasara a cikinsa a jiya da Yau Don kanawan zuma ce sai da Wuta.

Don Haka nake kiran Ma’abota Social media da mu fara wani Gangami na CETO KANO har Mahukunta su waiwayi matsalar, kuma mu koma cikin unguwanni don nemo mafuta tare da hada Kai da yan Kato da Gora da tsoffin jami’an tsaro da du wani Mai Gudunmowar bayarwa kan lamarin ya gagari Kwandila kar mu manta dole mu sanya DPO na yankinmu Don gudun taka Doka, Kai amfani da shafinka Don nuna takaicin abin da ke faruwa,ko kai sharing na rubutun wani ko Kai tagging na kanka har sakon ya isa gun Mahukunta, kar ka raina Gudunmowarka Dan uwa ka himmatu maza-maza Mutum Daya ya fadawa Goma.

Ibrahim mu’azzam Senator +234 703 861 7272