Jose Peseiro ya zama kocin Super Eagle
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta tabbatar da nadin Jose Peseiro dan kasar Portugal a matsayin sabon kocin Super Eagles kwanaki kalilan kafin a fara gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka.
Pesseiro mai shekaru 61 a duniya shi ne kocin ‘yan wasan kasar Portugal kan ya maye gurbin Gernot Rohr j bajamushen da NFF ta kora a watan jiya, sai dai hukumar kwallon ta Najeriya ta ce sabon kocin ba zai jagoranci ‘yan wasan Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fafata a Kamaru ba, inda Augustine Eguavoen da ke a matsayin kocin rikon kwarya zai jagoranci tawagar ta Super eagles.
A ranar 9 ga watan Janairun 2022 ne kasashen Afirka za su fara karawar neman cin kofin nahiyar a Kamaru, inda Najeriya ke a rukuni daya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bisau.