Jiragen yakin sojojin Najeriya sun kaddamar da hare-hare kan mayakan kungiyar ISWAP

Rahotanni daga Najeriya na cewa jiragen yakin sojojin Najeriya sun kaddamar da hare-hare da dama kan maboyar mayakan kungiyar ISWAP a arewa maso gabashin kasar.

Bayanai sun tabbatar da cewa jiragen, kirar Super Tucano mallakin rundunar sojin sama ta kasar, sun kashe kwamandojin kungiyar ta ISWAP a Kirta Wulgo da ke jihar Borno a wannan makon.

Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da jami’an tsaron kasar, ta rawaito cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar babban Kwamandan kungiyar mai suna Mallam Ari da ke lura da yankin na Kirta Wulgo.

“Wani babban jami’in rundunar sojan Najeriya ya ce hare-haren ta sama, wadanda aka kaddamar bayan an samu bayanan sirri, sun tabbatar da mutuwar fiye da ‘yan ta’adda 40 wadanda suke taruwa a gefen arewa maso gabashin Kirta Wulgo, kusa da inda aka dasa tutar wadanda ake zargin ‘yan ISWAP ne,” a cewar jaridar.

Kazalika, jiragen yakin sun kashe sojojin-haya da ke kera wa mayakan ISWAP bama-bamai.

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da kai hare-haren ta sama a yankin na Kirta Wulgo, bai ce komai ba game da yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

A baya dai, jami’an tsaro sun sha yin ikirarin nasara kan mayakan Boko Haram da ISWAP.

Ko da a karshen shekarar 2021, rundunar hadin gwiwa da ke aiki a yankin Tafkin Chadi ta ce dakarunta sun kashe mayakan ISWAP akalla 22, yayin da aka kashe sojojinta shida a wani artabu a Najeriya.